GWAMNATIN NASARAWA ZATA KORE DUK LIKITAN DAKE AIKI DA GWAMNATI KUMA YAKI ASIBITI MAI ZAMAN KANTA

Gwamnatin Nasarawa zata kore likitocin dake aiki a Asibiti mai zaman kanta

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kuddurin aniyar korar duk wani malamin kiwon lafiya dake aiki da Gwamnatin jihar kuma yake aiki a wani Asibiti mai zamna kan ta a fadin Jihar.

A zantawa da manema labarai a gidan Gwamnati dake garin Lafia a ranar Juma’a 28/8/2020 da misalin karfe 1:45 bayan tattaunawar da Gwamnatin ta gabatar.

Kwamishinan Shari’a Abdulkarim Kana tare da Kwamishinan yada labarai Dan Ladi Doga Shama. Suka shedawa manema labarai manufar Gwamnatin jihar na korar duk wani Likitwn dake aiki a Asibitin Gwamnatin jihar kuma yake da wani Asibiti ko aiki a wani Asibiti mai zaman kan ta.

Gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne saboda gyara matsalolin da ake samu a Asibitocin. Kuma Gwamnatin ta shirya samar da wada tattun likitoci yan asalin jihar.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta shirya baiwa duk wani Dan asalin jihar tallafi da za su yi karatun kiwon lafiya saboda su zama masu aiki a Asibitocin Jihar Nasarawa.

Gwamnatin ta ba da zabi ga duk wani malaman kiwon lafiya dake aiki karkashin Gwamnatin jihar da su zabe gurin daya ko aiki a Asibitin Gwamnati ko kuma mutum ya san matsayin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *