Gwamnatin jihar Nasarawa zata dauki tsatsauran mataki kan tsaftar muhali
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnatin jihar Nasarawa ta tabbatar wa al’umman Jihar cewa zata dauki kwakwarar mataki ga masu keta dokar tsafatar muhali na karshen wata.
Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Mazaber Obi Honorabul Iliya jekaba ya bayyanawa manema labarai bayan kammala dokar na wannan watan.
Hon. Iliya ya ce mafi yawan mutani suna ketare dokar shara da ake gudanarwa duk Asabar na karshen wata. Ya ce taimakon mutani su tsaya su share gidajen su ta yadda zai su kawar da gurbataciyar yanayi wanda zai kawar da cututuka.
Amma sai kaga mutani ba suyin sharar sun bige da yawace yawace a kan tituna.
Ya ce, Gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da dokar shara na tsarin mulkin 1999 kuma ya wajaba duk wani Dan Jihar ko wanda yake gudanar da ayyuka a cikin Jihar ko mai wacewa ya dakata ya bi dokokin da Jihar ta shinfida ko Kuma ya fuskanci hukunci.
Ya qara da cewa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya sanaya hannu kan amin cewa da dokar shara ya zama wajibi mutani su kiyaye dokoki kuma duk wanda aka kama shi yana yawo a lokacin dokar shara zai yabawa aya zaki.
Shima babban Jami’i a ma’aikatan tsafatar muhali ta jihar Nasarawa Alhaji Abubakar Muhammad ya jaddada wa al’umman Jihar matakin da Gwamnati ta dauka kuma ya qara da cewa yanzu sun kama mutum 27. Kuma daga yanzu za a cisu tara daga naira N5000 zuwa N10,000