SAMAR DA KANANAN SANA’O’I ZAI KAWO KARSHEN MATSALAR ALMAJIRANCI A NIJERIYA

SAMAR DA KANANAN SANA’O’I ZAI KAWO KARSHEN MATSALAR ALMAJIRANCI A NIJERIYA

Inji UNICEF

Daga Zubairu M Lawal

Wasu dsga cikin yaran da suke yawon barce barace a tutuna da sunan almajiranci sun amfana da sana’ar hannu da zai taimakawa rayuwar su.

Hukumar kula da qananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta ce hanyar da za abi a hanna yara qanana yawon barace barace da sunan almajiranci shine a samar masu da kananan sana’o’i da zasu suyi.

Ta ce kananan sana’o’i zai taimakawa rayuwar su zai kuma basu kwazo da kwarin giwa wajen gudanar da karatu a zaune waje daya.

Ta qara da cewa wajibine a samarwa yaran da kananan sana’o’i da zai taimaki rayuwar su ya basu damar kulawa da kansu.

Yau a tarayyar Nijeriya mahukunta sun dukufa wajen dakile yaduwar yara kanana a kan tutuna da suke yawon barce barace da sunan almajiranci.

UNICEF tace hanyar da ya dace abi shine a samar da fannonin sana’o’i hannu a cikin makarantun na su a samar da malaman da zasu riqa koyar da su sana’o’i suna kuma karatu a dukkan fannonin Ilumi.

Tace yanzu rayuwar Mohammed yayi kyau yana alfahari da kansa a matsayin yaro da yake dogaro da abinyi ba sai yaje yayi bara ba.

Mohammed ya koyi sana’ar Saka a a cibiyar koyar da sana’o’i na yara Kuma yana karatu allo a lokaci guda ba saki daya ba ya hada duka ya na yi.

Saboda karatu da Sana’a duka ribar sa ne. Kuma zai girma cikin mutanin da suke da abinyi zai taimakawa dangin sa.

Cikin wannan shekarar da muke ciki Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abdullah Umar Ganduje ta kudduri aniyar cigaba da kula da almajirai ta hanyar kulawa da karatunsu da kuma zamanatar da zaman takewar su.

Zasu kasance masu yin karatun addini da na zamani sannan ta samar da fannin koyan sana’o’i da za a riqa koyarwa saboda yaran su koya su kuma dogara da kansu.

Fannin karatun allo ya samu tarihi a kasar nan tsawan shekaru ba abune da za a kawar da shi ba. To amma zamani ya sauya da za a iya zamanatar da shi yaro yakan iya yin karatu a gaban iyayen sa.

Yayi karatu ya hada da sana’a irin wanda ya ke so saboda zai taimakawa rayuwar sa, ba tare da yayi bara a titi ba.

Hukumar kula da yara qanana UNICEF ta koyar da yara kanana sana’o’i kala dabam dabam kuma yanzu yaran suna jin dadi yadda suka samu aikin yin a hannun su.

Kuma zai rage masu radadin talauci da yawo a kan tituna da sunan barace barace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *