SAMAR DA TSAFTACECEN RUWAN SHA ZAI KAWO KAR SHEN MATSALAR COVID-19 A SANSANIN YAN GUDUN HIJIRA

SAMAR DA TSAFTACECEN RUWAN SHA ZAI KAWO KAR SHEN MATSALAR COVID-19 A SANSANIN YAN GUDUN HIJIRA

Inji Jami’an kiwon lafiya

Daga Zubairu M Lawal

Jami’an kiwon lafiya dake kula da al’umman dake zaune a sansanin yan gudun Hijira dake yankin Jihar Borno dake Arewa maso gabashin Nijeriya sun bayyana matsalar ruwan sha mai tsafta zai kara samar da yawai tar cututuka a yankin.

Sun bayyana yadda annobar cutar Korona bairus ke yaduwar cukin mutani kamar walkiya. Amma yawan jama’an dake rayuwa a sansanin yan gudun Hijira suna fuskantar barazanar matsalar ruwan sha mai tsafta.

Hukumar shiga da fice da malaman kiwon lafiya dake kula da mazauna sansanonin dake yankin sun bayyana cewa samar da tsaftacecen ruwan sha zai taimaka wajen kawo karshen annobar cutar Korona bairus da sauran cututuka dake yaduwa.

Hukumar ta bayyana cewa akasarin al’umman dake rayuwa a jihar Borno suna zaune ne a sansanin yan gudun Hijira saboda matsalar tsaro.

Sukace kimanin mutanin jihar kashi 80 suna rayuwa ne a sansanin yan gudun Hijira dake yankin.

Kusan mutum 840,000 suke zaune a sansanin saboda matsalar rashin tsaro da rigin gimun yan Ta’adda da su ke kai hare hare kauyukan da jama’a ke zaune.

Mahukuntan sun bukaci a kara samar da guraren ruwan sha mai tsafta. Saboda magance yaduwar annobar cutar Korona bairus wanda yakeyin dauki dai dai a cikin sansanonin.

Ko a kwànakin baya cutar ta rika farma yara kanana da mata amma jami’an kiwon lafiya dake yaki da yaduwar annobar cutar Korona bairus suna kawo agajin gaggawa.

Mahukuntar sun bukaci a gaggauta karo kayan yaki da cutar wannda zai wadace al’umman dake rayuwa a sansanonin saboda al’umma na kara yawaita ne a sansanonin sakamakon hare haren da yan Ta’adda ke kai wa.

Kuma kowa ya san Jihar Borno tana cikin jihohin da annobar cutar Korona bairus ta shige ta kuma kullun ana kara samuwar masu cutar a jihar.

Wajibine a samar da garkuwan da zai kare al’umman dake zaune a sansanin yan gudun Hijira saboda kada na waje dake zuwa su shigo da cutar .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *