YAKI DA TA’ADDANCI KAKAKIN MAJALISAR NASARAWA YA JINJINAWA SHUGABAN BUHARI DA GWAMNAN NASARAWA

YAKI DA TA’ADDANCI KAKAKIN MAJALISAR NASARAWA YA JINJINAWA SHUGABAN BUHARI DA GWAMNAN NASARAWA

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah ya jinjinawa Shugaban qasa Muhammad Buhari da Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule bisa himma da sukayi na tarwatsa Rundunar yan Ta’adda a jihar Nasarawa.

Honorabul Balarabe Abdullah ya ce wannan nasarar da Rundunar Sojojin Nijeriya sukayi ya samo asali ne ta kokarin da Gwamnati tayi.

Ya ce Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya baiwa vangaren tsaro mahimmanci saboda ganin al’umman Nijeriya sun samu kwanciyar hankali.

Ya ce wannan nasarar abin jinjina ne ga Gwamnatin Muhammad Buhari saboda bashi da wani kudduri face yaga an samu zaman lafiya a tarayyar Nijeriya.

Kakakin Majalisar ya ce tarwatsa Rundunar yan Ta’addan Darul-salam babban fannin nasara ne da Gwamnatin Buhari da na Gwamna Abdullah Sule.

Ya yabawa Gwamna Abdullah Sule saboda tunda ya kama ragamar mulkin Jihar Nasarawa ya ke ta kokarin a samar da dauwamamiyar zaman lafiya.

Ya kara da cewa tarwatsa Rundunar yan Ta’addan Darul-salam da akayi a Uttu zai samar da zaman lafiya mai durewa da aminci a yankin karamar hukumar Toto da ma jihar Nasarawa.

Kakakin Majalisar ya ce zaman yan kungiyar Darul-salam babban barazana ne a yan kin qaramar hukumar Toto da jihar Nasarawa.

Saboda al’umman yankin sun kasa samun zaman lafiya sakamakon zaman wadannan kungiyoyin a yankin. Tashin hankali fashi da makami Garkuwa da mutani a neme kudin fansa da hare-hare na ta’addanci sun yawaita a yankin Toto.

Honorabul Balarabe Abdullah ya jinjinawa Rundunar Soja ta masamman kan yadda suka fadada ayyukan su har zuwa yankin Jihar Kogi da Niger inda sukayi tankade da rairaya suka kamo yan Ta’addan da suke hana al’umma zaman lafiya da yawan su ya kai 410 a ranar 25/8/2020.

Sannan ya kara kira ga Rundunar Soja da su kara kaimi wajen yaki da duk kungiyoyin yan Ta’adda dake Jihar. Ya kuma bukaci al’umman Jihar da su baiwa Rundunar tsaro hadin kai wajen magance duk wasu yan Ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *