MAJALISAR DINKIN DUNIYA ZATA TAIMAKAWA NIJERIYA WAJEN YAKI DA KORONA DA KUMA HIV

MAJALISAR DINKIN DUNIYA ZATA TAIMAKAWA NIJERIYA WAJEN YAKI DA KORONA DA KUMA HIV

Daga Zubairu M Lawal

Nijeriya ta zata hada hannu da Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da cutar kanjama’u da na Annobar cutar Korona bairus.

A taron hadin giwa da akayi tsakanin mahukuntar Nijeriya da Jami’in Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da Annobobin da yake addabar al’umman Nijeriya.

Babban Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Mista Boss Gida Mustapha ya sheda cewa Gwamnatin tarayya zata hada hannu da Majalisar Dinkin Duniya wajen kokarin kawar da cututtuka masu karya garkuwan jiki da cutar sarke nunfashi.

Mista Boss Mustapha ya ce Gwamnatin Nijeriya tayi namijin kokari wajen dakile yaduwar annobar cutar Korona bairus a kan lokaci.

Saboda matakin da Gwamnati ta dauka na rufe iyakoki da kuma rufe garuruwa ya sanya  cutar Korona bairus bai samu damar yaduwa ko ta ina ba.

Ya qara da cewa dole a ya bawa Gwamnatin da jami’an yaki da cutar da likitocin Nijeriya da suka sadaukar suka ba da lokaci wajen ganin an dakile yaduwar annobar Korona bairus.

Shima Minstan kiwon lafiya ta Nijeriya Dakta Osagie Ehanire ya ce Nijeriya batayi wasa ba ta mike tsaye tun a lokacin da cutar ta billo kai cikin watan fabirerun shekara ta 2020.

Ya ce a lokacin da cutar ya riqa yaduwa a yan kin Jihar Lagos da sauran wasu jihohi Gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye wajen tsa da cutar.

Shima Darkta Janaral mai binciken cututtuka Dakta Chikwe Ihekweazu ya ce Gwamnati ba tayi jin kiri ba. Wajen yaki da cututtuka da suka hada da Annobobin da suke yaduwa.

Babban Kodineto na Majalisar Dinkin Duniya Mista Edward Kallon ya ce Majalisar Dinkin Duniya zata taimakawa Nijeriya wajen kawar da cututtuka da suka hada Kanjama’u da Korona bairus.

Dakta Fiona Braka ya ce hukumar kula da fannin kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya zata bada nata tallafin saboda ganin al’umma sun tsira daga cututtuka dake yaduwa a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *