BURINMU KYAUTATAWA AL’UMMAN MU DOMIN SAMUN WADATACEN ABINCI – AMINU MAI FATA

Shugaban Karamar Hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya kaddamar da motar Noma ga al’umman karamar hukumar Lafia a Jihar Nasarawa.

Shugaban Karamar hukumar ya ce yana alfahari da yankin karamar Hukumar Lafia manema ne.

Komai ya tabbatar da noman da zakeyi zai taimakawa al’umman Nijeriya. Wannan motar noman zai amfani manoman da karamar Hukumar Lafia

Da ya ke jawabin gaban dubban matasa da karamar Hukumar ta tallafa masu da farar riga da wando da takalmi wanda zasu koyi aikin Dan Sanda da shi a sansanin horar da sabin yan sandan. Aminu Mu’azu mai Fata ya ce Karamar Hukumar ta tallafa masu da wannan kayan ne saboda su san cewa Shugabannin Karamar Hukumar Lafia suna farin ciki da shigan su wannan aiki.

Ya bukaci dubban matasan da su zama jakadu na gari su kuma yi aiki tsakanin su da Allah kada suyi abinda zai zubar masu da daraja ko ya janyo akore mutum daga aiki.

Mai fata ya janyo hankali matasan da su zama wadanda zasu kare martabar Nijeriya a bakin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *