KAKAKIN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR NASARAWA YA BUKACI MATASA SU RUN GUMI ZAMNA LAFIYA DAN CIGABAN NIJERIYA

KAKAKIN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR NASARAWA YA BUKACI MATASA SU RUN GUMI ZAMNA LAFIYA DAN CIGABAN NIJERIYA

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah yayi kira ga matasan Nijeriya dadu guji tsoma kan su cikin ayyukan ta’addanci.

Honorabul Balarabe Abdullah ya bayyana haka ne sa’ilin da yake amsar lambar yabo na girmamawa da kungiyar Matasan Nijeriya mai suna ( Global Alliance of Northern Nigeria Youths) suka bashi a ofishin sa dake Majalisar dokokin jihar Nasarawa a garin Lafia.

Kakakin Majalisar dokokin ya bukace su dasu rungumi akidar zaman lafiya wanda zai samar da cigaba a rayuwar su da kuma bunkasa kasa.

Ya ce zaman lafiya shine babban kuddurin cigaban kowata al’umma da take tinkawo da cigaba.

Kakakin Majalisar ya jinjinawa matasa da suka hada kai domin cigaban wannan kasar da kuma zurfin tunanin da suke da shi na duba kyawawan ayyukan cigaban da wasu Shugabannin ke yi.

Ya ce watara matasan sune zasu jagoranci kasan nan saboda haka su sanya wa kawunansu tunani mai kyau domin Nijeriya tayi alfahari da su nan gaba.

Sannan ya yi kira ga matasa da su rika waiwayen masu tasowa suyi kokarin daurasu ana tubalin gaskiya ta yadda zasuci riban rayuwar su.

Ya ce akwai wadanda yanzu bukatar su shine ganin lalacewar matasan kasan nan. A duk lokacin da “muka rasa matasa masu zurfin tunanin cigaba to kasar mu ta fada cikin damuwa.

Saboda kowata qasa takan yi tinkaho da matasan ta masu kishin cigaban kasa ne, ba wadanda suka lalace ba.

Shima a nasa jawabin Sakataren kungiyar  Global Alliance of Northern Nigeria Youths.Kwamared  Mohammed Awal Abdullahi Ya yabawa kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa saboda yadda yake jagonatar Majalisar cikin kyakyawar tsari da yayi daidai da cigaban al’umman jihar.

Ya qara da cewa haka akeson Shugabanci,Shugaba ya zama mai aiwatar da kyawawan ayyukan cigaban al’umma.

Ya ce wannan kyawawan manufar na Kakakin Majalisar ne ya sanya kungiyar ta sanya shi cikin gwarazan da ta karramasu da lambar yabo.

Sannan ya kuma yaba da shawarar da Kakakin Majalisar ya basu na kaucewa tsoma kai cikin kungiyoyin Ta’addanci ko bata gari da ba zai haifarwa qasan nan ko mai ba sai koma baya.

Ya ce idan ” mu matasa muka kaucewa ayyukan asha da kungiyoyin Ta’addanci babu wanda ya isa yayi amfani damu da karfin tuwo. Kuma mune idan muka hada kai zamu kawo cigaba kowani iri a Nijeriya “.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *