SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR LAFIA AMINU MAI FATA YA BAIWA MATASA TALLAFI HAR DA MOTAR NOMA

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR LAFIA AMINU MAI FATA YA BAIWA MATASA TALLAFI HAR DA MOTAR NOMA

Daga Zubairu Lawal

Shugaban Karamar Hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya kaddamar da motar Noma ga al’umman karamar hukumar Lafia a Jihar Nasarawa.

Shugaban Karamar hukumar ya kaddamar da motan ne a ranar Laraba a harabar Sakatariyar. ya ce yana alfahari da al’umman yankin karamar Hukumar Lafia saboda manoma ne.

Shugabn karamar Hukumar ya tabbatar da noman da a zakeyi zai taimakawa al’umman Nijeriya. Wannan motar noman zai amfani manoman da ke noma a dukkan karamar Hukumar Lafia.

Samar da ire-iren wannan taimako ne ga al’umman karamar Hukumar Lafia da daga darajar karamar Hukumar wajen samar da wada taccen abinci.

Da ya ke jawabin gaban dubban matasa da karamar Hukumar ta tallafa masu da farar riga da wando da takalmi wanda zasu koyi aikin Dan Sanda da shi a sansanin horar da sabin yan sandan.

Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya ce Karamar Hukumar ta tallafa masu da wannan kayan ne saboda su san cewa Shugabannin Karamar Hukumar Lafia suna farin ciki da shigan su wannan aiki.

Ya bukaci dubban matasan da su zama jakadu na gari su kuma yi aiki tsakanin su da Allah kada suyi abinda zai zubar masu da daraja ko ya janyo akore mutum daga aiki.

Mai fata ya janyo hankali matasan da su zama wadanda zasu kare martabar Nijeriya a bakin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *