GWAMNATIN TARAYYA TA UMURCI MAKARANTU SU FARA SHIRIN KOMAWA

GWAMNATIN TARAYYA TA UMURCI MAKARANTU SU FARA SHIRIN KOMAWA

Gwamnatin tarayya ta umaurci daukacin jihohin kasar nan da su fara shirin bude makarantu don ci gaba da harkokin karatun dalibai.

Babban jami’in kwamitin fadar shugaban kasa na karta kwana dake yaki da cutar COVID-19 Dakata Sani Aliyu ne ya bayyana hakan, yayin da yake wata tattaunawa da manema labarai a fillin jirgin saman Nmandi Azikwe dake birnin tarayya Abuja.

Dr. Sani Aliyu na cewa shakka babu ya gamsu da yadda ake ciki a yanzu haka, wanda la’akari da kyautuwar yanayin ne ya sa ya bada umarnin.

Matakin bude makarantun dai ya shafi makarantun raino na Nursery da Firamare da Sakandare da kuma na gaba da Sakandare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *