AN SAMU SAMA DA MUTUM 400 MASU CUTAR COVID-19 A JIHAR NASARAWA

AN SAMU SAMA DA MUTUM 400 MASU CUTAR COVID-19 A JIHAR NASARAWA

 

Inji Kwamishinan Lafiya

 

Daga Zubairu  Lawal

 

Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Famasi Ahmad Baba Yaya ya bayyana wa manema labarai haka a ofisinsa dake garin Lafia.

 

Kwamishinan ya ce a dukkan  gwaje gwajen da Gwamnatin jihar tayi domin dakile yaduwar annobar cutar Korona bairus a Jihar a kalla anyiwa kimanin mutani 3509 a Jihar.

 

Ya ce an kuma samu masu dauke da cutar Korona da yawansu ya kai kimanin 400 da wani abu. Kuma an kwantar da su a Asibitocin da aka kebe domin jinyar masu dauke da kwara Annobar cutar.

 

Bayan basu kulawa da magunguna mutum 350 sun samu lafiya har an sallamisu sun koma gidajen su. Sannan kimanin mutani 13 suka rigayemu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da wannan cutar cikin su harda Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa.

 

Yanzu akwai mutum 16 da suke kwance a Asibiti suna karban magani duk wanda yaji sauki muna sallamar sa ya tafi gida ya cigaba da aikin sa . akwai wadanda suna gidajen su amma nana kara bibiyansu muna duba jikinsu.

 

Idan ka duba zaka ga cewa Gwamnatin jihar Nasarawa tayi matukar kokari wajen dakile yaduwar annobar cutar a cikin Jihar. Kuma jihar tayi na mijin kokari wajen kulawa da al’umman jihar domin samar da kariya domin dakile yaduwar cutar.

 

Kwaminshinan ya kara da cewa duk ma’aikacin jinya dake kar kashin Gwamnatin bai kamata ace lokacin aiki ya bar Asibiti ya je wani guri na kashin kan sa ba .

 

Zamu sanya ido duk wanda muka kamashi ya bar Asibiti a lokacin aikin sa yaje wani Asibiti ko nashi ko na yan kasuwa yana aiki a cikin lokacin aikin Gwamnati zamu hukunta shi.

 

Mun san cewa aikin Asibiti yana da vangarori da yawa amma dole ne malamin jinya ya tsaya a bakin aikin sa har sai lokacin tashin sa yayi sai yaje wani gurin da yake aiki.

 

Wannan dokan aiki ne a ko ina ba sabon tsari bane kuma zamu tsaya tsayin daka mutabbatar da anyi amfani da wannan dokar a dukkan Asibitocin Gwamnatin jihar Nasarawa.

 

Komai yana da dokoki sai dai akwai kwararun Likitocin da dole ka kyalesu saboda ana bukatar su a ko ina kuma ireirensu basu dayawa a yanzu kuma aikin da sukeyi ba kowa ne ke iya yi ba.

 

Idan mutum ya tashi daga aiki domin kowani aiki akwai tsarin awowin da ma’aikaci zai dauka a bakin aiki. Idan mutum ya tashi a madadin ya je gida kawai ya kwanta yana iya zuwa wani gurin yayi aiki saboda qasan nan an fama da karancin Malaman kiwon lafiya ko ta ina.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *