KO KUNSAN SUWAYE – MUTUNI TARA DA AKA YANKEWA HUKUNCIN KISA A JIHAR KANO DAKE AREWACIN NIJERIYA

KO KUNSAN SUWAYE – MUTUNI TARA DA AKA YANKEWA HUKUNCIN KISA A JIHAR KANO DAKE AREWACIN NIJERIYA

Husaina Yusuf Kano

Baya nai nuni da cewa mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Agustan 2020.

Takardun kotuna daban-daban da BBC Hausa ta samu sun nuna cewa an yanke hukunce-hukunce kan mutanen ne bayan samunsu da hannu a aikata mabambanta laifuka.
An samu bakwai daga cikinsu da aikata kisan kai, mutum ɗaya ya aikata fyaɗe yayin da aka kama ɗaya da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

A makon jiya ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin sanya hannu kan takardar kashe Yahaya Sharif-Aminu, mutumin da aka samu da laifin batanci ga Annabi.

An yanke hukuncin farko ne ranar 11 ga watan Fabrairu, inda za a kashe Ali Abdullahi ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan kai.

Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan:

Ali Abdullahi
Kotu mai lamba Shida ta kama shi da laifin kisan kai inda ranar 11 ga watan Fabrairu aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Yakubu Ɗalha
Shi ma Yakubu Kotu mai lamba Shida ce da ke birnin Kano ta kama shi da laifin kisan kai, kuma ranar 3 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Abdullahi Isyaku
Babbar Kotun Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 16 ga watan Maris.

Mujahid Sa’id
Kotu mai lamba 13 ta same shi da laifin kisan kai inda a ranar 24 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *