SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR LAFIA YA KADDAMAR DA KWAMITIN YAKI DA AJIYAN MOTOCI A MANYAN TITUNA DA NA HARKAN NOMA

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR LAFIA KADDAMAR DA KWAMITIN KULA DA NOMA

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Shugaban karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya kaddamar da kwamitin harkan noma ga al’umma karamar hukumar Lafia.

Da yake jawabi Shugaban karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya ce karamar hukumar Lafia tana da kishin samar da wadacecen abinci da zai amfani al’umman jihar Nasarawa.

Ya ce Sun ware zunzurutun kudi sun saye sabon motar Noma sannan an gyara  tsohon motar Noma da take kasa   saboda suyi aikin da zai samar da abinci masamman a wannan lokacin da ake fama da bukatar abinci mai gina jiki.

Shugaban karamar hukumar ya qara da cewa wannan motar mallakin karamar hukumar ce kuma duk wani mazauni karamar hukumar Lafia yana da haki matukar zaiyi noma.

Ya ce , an sanya farashi dabam dana yan kasuwa an saukaka abin da mutani zasu biya idan suna bukatar aiki da motar noman.

Ya bukaci kwamitin da su sanya ido sosai wajen kulawa da wannan motar noman saboda an samar da shine saboda saukaka wa manomar karamar hukumar.

Kuma su kulla da gyransa kamar nasu mallakin kansu. Kafa su zura ido subar kowa yayi abinda yaga dama dashi yace kayan Gwamnati ne.

Shugaban karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya ce kamar yadda yake gudanar da aiki a kullun haka zai cigaba da sanya ido wajen ganin anyi tattalin da kaddarorin karamar hukumar saboda na al’umman karamar hukuma ne kuma shi Shugaba ne .

Ya kuma janyo hankalin kwamitin da su riqa ajiye kudaden da motocin sukayi aiki a cikin asusu Gwamnati na masamman da aka ware domin aikin motocin Nomar, saboda nan gaba ana da bukatar samar da wasu abubuwan da zasu taimaki al’umman karamar hukumar.

Haka zalika an kaddamar da kwamitin kula da ajiyar motoci a gefen tituna.

Shugaban karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu mai Fata ya kaddamar da kwamitin karkashin Jagorancin Hukumar kiyaye hadura ta qasa reshen Jihar Nasarawa.

Kwamitin dake dauke da Hukumar Yan sanda da DSS da NSCDC da NAYES da NUDB da Ma’aikatan karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar ya janyo hankali kwamitin da suyi aiki domin kare al’umman jihar daga hadarorikan yan Ta’adda dake fakewa da ajiyan motoci suke aikata miyagun laifuka.

Ya ce masu sauke fasinjoji a bakin titi suna haddasa cin koso akan manyan hanyoyi. Kuma suna lalata kwalbatocin da Gwamnatin jihar ta kashe makudan kudi ta yi su.

Ya ce a kwanaki Gwamnan jihar Injiniya Abdullah Sule sai da yayi magana saboda masu ajiye motoci sun lalata kwalbatin gefen filin taro dake wajen.

Ya ce , dole mukaje muka kara kashe kudi muka gyra gurin..

Mai Fata yace wannan shine makasudin kafa wannan Rudunar ta masamman da zasu kula da masu sauke fasinjoji ko masu ajiye motoci a gefen titi ko masu barin mota a titi idan ta lalace.

Ya yi kira ga jama’a dasu kiyaye saboda duk Wanda aka samu da wannan laifin za’a hukunta shi. Gwamnatin jihar baza ta kyale duk Wanda aka kama ba.

Ya ce Lafia itace Babban birnin jihar Nasarawa bai kamata a sameta da irin wannan cin koso ba. Kuma mutani suna zube shara a magudanar ruwa na manyan tituna shuma duk wanda aka samu da wannan zai yabawa aya zaki.

Dole duk wadanda suka gudanar da harkoki a gefen tituna su kula da tsaftace muhalin da suke zaune saboda gyara babban birnin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *