AN BUKACI GWAMNONI SU BAIWA YAN MAJALISAR DOKOKIN JIHOHI HAKIN SU -PASAN

Ya kamata Gwamnoni subi umurnin tarayya ta baiwa Majalisar dokokin cin gashin kansu

Shugaban PASAN

Daga Zubairu M Lawal

Shugaban kungiyar Majalisar dokokin ta jihohin Nijeriya Kwamared Muhammad Usman yayi kira ga gamayyara Gwamnonin Nijeriya da su bi Umurnin Majalisar tarayya da Gwamnatin Tarayya kan baiwa Majalisar dokokin cin gashin kansu.

Da yake jawabi a lokacin da tawagar ya’yan kungiyar suka ziyarci Majalisar dokokin ta Jihar Nasarawa Kwamared Muhammad Usman ya ce, dangane da kuddurin da dokar kasa ta bada na baiwa Majalisar dokokin jihohin kudaden su kai tsaye saboda gudanar da ayyukan Majalisa.

Ya ce, Majalisar dokokin tana da ayyukan da take da ikon gabatar dasu ba tare da Gwamnan jihar ya amince ba.

Kuma dokane Majalisar dokokin ta Jihar ta rika karban kasunta na kudade kai tsaye ta kuma gudanar da ayyukan Majalisar kai tsaye ba tare da sai Gwamnan jihar ya amince ba.

Ya ce , a kwanaki Gwamnatin Tarayya karkashin Jagorancin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya rattaba hannu akan Majalisar dokokin ta jihohin su zama masu cin gashin kan.

Kwamared Muhammad Usman ya qara da cewa matukar Gwamnonin jihohin suka kibin wannan umurnin to kungiyar zata saya kafar wando daya da kowani Gwamnan jihar.

Ya ce , tun tuni aka tabbatar da wannan dokar amma sunji suru Gwamnonin basuyi wani abuba. Shi ya sanya kungiyar ta fara tuntubar yan Majalisar dokokin ta jihohin saboda ta sanar da ita da kuma irin matakin da zata dauka.

Ya ce , mun farane da Jihar Nasarawa. Shima a nasa jawabin Shugaban Majalisar dokokin jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah Wanda ya samu wakilcin mukaddashin Shugaban Majalisar Hon. Nehemiah Tsentse Dandaura ya yabawa kungiyar (PASAN) game da wannan Gwagwarmayan da suka miqe tsayi sukeyi.

Ya Kuma yaba da Jagoranci irin na Shugaban kungiyar Kwamared Muhammad Usman da yadda yake jajircewa kan duk kuddurin Majalisar dokokin ta jihohin Nijeriya.

Ya kuma bukaci kungiyar da ta qara himma kuma a tafiyar da abubuwa bisa tsari domin cimma xa mai ido cikin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *