CIGABA – JAMI’AR MARYAM ABACHA TA BAIWA JAMI’AR FUDMA KYAUTAR BABBAN MOTA

Jami’ar Maryam Abacha Ta Bai Wa Jami’ar FUDMA Kyautar Babbar Mota

Hukumar jami’ar Maryam Abacha American University, dake Maradin Jamhuriyyar Nijer (MAAUN), ta bai wa Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina kyautar babbar mota kirar Bas mai daukar mutum 60.

Da yake mika wa shugaban jami’ar ta FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi makullan motar a ranar Lahadi a garin Dutsinma, shugaban jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo, ya ce sun bayar da wannan tallafin ne ga jami’ar a wani mataki na bai wa jami’ar gudummawa wajen ci gaban ilimi a kasarnan.

Dr Aliyu Haruna, shi ne ya wakilci Farfesa Gwarzo, ya kuma tabbatar da cewa tallafin zai taimaka wajen zirga-zirgar dalibai da ma’aikatan Jami’ar. Ya kara da cewa; Jami’ar MAAUN za ta ci gaba da bunkasa alakar dake tsakaninta da Jami’ar FUDMA domin ganin ta cimma manufar kafa jami’ar.

Da yake maida jawabi, shugaban Jami’ar FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi, ya jinjinawa mu’assasin Jami’ar MAAUN dake jamhuriyyar Nijer, Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo bisa wannan tallafi da ya ba su.

“A madadin shugaban hukumar gudanar da Jami’ar FUDMA, Alhaji Uba Ahmed Nana, hukumar jami’ar, ma’aikata da dalibai na jami’arnan, a yau na karbi makullan mota daga hukumar gudanar da jami’ar Maryam Abacha American University, Maradi a karkashin shugabancin Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo” In ji shi.

Ya kara da cewa; za su tabbatar da an yi amfani da motar bisa turbar da aka bayar wajen rage wa dalibai da ma’aikata radadin zirga-zirga. Har wala yau ya jinjinawa Abubakar-Gwarzo bisa gudummawar da ya bai wa jami’ar ta hanyoyi daban-daban, inda ya ce jami’ar FUDMA za ta ci gaba da karfafa alakarsu wajen ci gaban ilimi a Nijeriya.

“Mun ji dadi bisa wannan tallafin da ku ka bamu domin hakan zai taimakawa jami’armu ta hanyoyi da dama. Kuma kamar yadda ya yi alkawari, tuni ya fara tallafa mana wajen yi wa jami’ar FUDMA rijista da UNESCO”. Ya tabbatar.

Ya kara da cewa; “kuma ya yi alkawarin taimaka mana wajen horas da ma’aikatanmu a birnin Paris a duk lokacin da muka kafa sashen koyar da harshen Faransanci”.

A karshe ya tabbatar da cewa jami’ar a shirye take wajen kulla alaka da Jami’ar MAAUN a bangaren da ya shafi horaswa, bincike da kuma ci gaba wajen bai wa jami’o’in biyu damar karawa da sauran takwarorinta na kasarnan da ma sassan duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *