KO KUNSAN – DALILIN DA YASA AKA SAMAR DA SARAUTAR GIWAR MATAN JIHAR NASARAWA?

KO KUNSAN – DALILIN DA YASA AKA SAMAR DA SARAUTAR GIWAR MATAN JIHAR NASARAWA?

Daga Zubairu Lawal

A makon da ya gabatane Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa Mai Shari’a Dauda Sidi Bage ya nada Uwargidan Gwamna Jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule a matsayin Giwar Matan Jihar Nasarawa.

Hakika masu ruwa da tsaki gida da waje sun hallara a wajen bukin wankan Sarautan Giwar Matan Jihar Nasarawa.

Hajiya Silifat Abdullah Sule Uwargidace ga Gwamnan jihar Nasarawa kuma ta taka mahimmiyar rawa wajen ganin cigaban Matan Jihar Nasarawa a shekara guda da watanni da suka kasance a bisa kujerar mulkin Jihar Nasarawa.

Hajiya Silifat Abdullah Sule ta taka mahimmiyar rawa wajen yaki da masu cin zarafin mata a fadin Jihar.

Ta kasance macen da ta dauki alkawarin koda zatayi yawo a kasa babu takalmi sai an biwa jaririya yar wata uku hakinta na Fyade da akyi mata. Wannan matakin da Uwargidan Gwamna ta dauka ta samu yabo gida Jihar Nasarawa da Nijeriya da kasashen waje .

Da ire-iren wadannan ayyukan ya sanya Mai Martaba Sarkin Lafiyan Bare-bari ya nada ta sarautar da yafi kowanne girma wato GIWAN MATAN JIHAR NASARAWA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *