Annobar cutar Korona bairus ya kawo na kasu ga bukin ranar Ma’aikatan jiragen ruwa – MDD

Annobar cutar Korona bairus ya kawo na kasu ga bukin ranar Ma’aikatan jiragen ruwa

MDD

Daga Zubairu Lawal

A sakon da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres ya aikawa ilahirin Ma’aikatan jiragen ruwa ta Duniya dan gane da ranar da aka kebe dumin gudanar da bukukuwar ranar Ma’aikatan jiragen ruwan.

Ya jinjina masu dangane da ayyukan da sukeyi na kokarin yaki da annobar cutar Korona bairus.

Mista Antonio Guterres ya ce annobar cutar Korona bairus ta dakile hanyoyin cigaba a Duniya ta ko ina ciki harda tashoshin jiragen ruwa ta Duniya annobar bata bari ba.

Babban Sakataren ya jinjinawa Ma’aikatan jiragen ruwa bisa yadda suke gudanar da ayyukan su cikin nasara.

Ya ce aikin jiragen ruwa aikine na sufuri mai dake tafiyar da harkoki dabam dabam a fadin Duniya.

Kuma tana da ma’aikata da miliyoyin ma’aikata a kowani gabar teku dake fadin Duniya.

Ana samun cigaba da hada hadan harkokin kasuwanci tsakanin qasa da kasa ta hanyar sufurin jiragen ruwa.

Babban Sakataren ya ce , a lokacin da ake ciki na annobar cutar Korona bairus an samu na qasu so sai sakamakon rashin zurga zurgan da jiragen ruwa ba suyi tsakanin kasa da kasa.

Kasa shen Duniya da dama sun shiga cikin halin kunci sakamakon rashin zurga zurgan jiragen ruwa saboda komai ya tsaya al’umma suna zaune a gidajen su. Babu harkokin hada hada Korona bairus ta tsai da komai a fadin Duniya.

Mista  Guterres yayi kira ga Gwamnatocin qasashen Duniya dasu daura damarar yaki da harkwn safarar mutanin da ke zuwa cirani a Kasashen Turai.

Ya ce akasarin masu zuwa ciranin suna amfani ne da kananan jiragen ruwa zuwa kasashe masu nisa daga bisani akan samu matsala ta kan kai ga asarar rayuka.

Wasu lokutan manyan jiragen ke ceto mutanin da suka fada cikin hadarin igiyan ruwa Dan haka ya qara jin jinawa Ma’aikatan dake aiki a jiragen ruwan.
 

,
 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *