AN KAMA MUTUM 67 DA SUKA KETA DOKAR TSAFTAR MUHALI A NASARAWA

An kama mutani 67 da suka keta dokar shara a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnatin jihar Nasarawa ta tabbatar da kama mutani 67 da suka keta dokar tsaftar muhali ta qar shen wata da akeyi.

Da yake zantawa da manema labarai Alhaji Abubakar Muhammad Darakta a Ma’aikatan tsaftar muhali ya ce , Gwamnatin ta kama mutani 67 da suka keta doka suka fito suna gudanar da ayyukan su a ranar dokar shara.

Ya ce , mutanin da aka kama akasarinsu ba yan Jihar Nasarawa bane wadanda suka shigo Jihar ne da nufin yin Zanga zangar End#SARS.

Da zanga zangar ya gagara yuhuwa sakamakon Matasan Jihar Nasarawa sunki ba da hadin kai sai sukayi zaman su. Daraktan ya ce, sun ganosu ne ta hanyar cewa basu San da wannan dokar ba.

Wannan ya nuna cewa ba yan asalin Jihar Nasarawa bane.

Ya ce ana kama abeben hawa kuma Gwamnatin tana tafiya da Kotun tafi da gidan ka, duk Wanda aka samu da laifi akwai hukunci tara daga #5000 zuwa sama.

Dai dan lefi dai dan tara da za’ayiwa wanda aka kama. Ya ce daga wata mai kamawa hukumar kula da tsaftar muhali zata rika shiga gida -gida  domin tabbatar da anti shara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *