ZA A BAIWA LIKITOCI HURO NA MUSAMMAN DOMIN KULAWA DA AL’UMMAN AREWA TA GABAS -EDWARD KALLON

Za a baiwa likitoci huro na masamman domin kulawa da al’umman Arewa ta gabas

Inji Edward Kallon

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Hukumar kula da kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara shirin horar da Malaman kiwon lafiya dake aiki a sansanonin yan gudun Hijira dake yan kin Arewa ta gabas horo na masamman domin kula da lafiyan su.

Babban kodineta a tsare -tsaren ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Mista Edward Kallon ya bayyana haka.

Ya ce akwai Malaman kiwon lafiya da suka hada da Likitoci da Nursi da suke aiki a wajen saboda haka za a kara masu horo domin samu cigaba kan ayyukan su.

Ya ce cikin Malaman kiwon lafiya akwai maza da mata da yan mata saboda haka suna bakin kokarin su to amma za a rika horar da su a kai akai saboda samun gogewa a bakin aiki.

Mista Edward Kallon ya bayyana wa Ma’aikatan kiwon lafiya dake aikin ceton rai a yan kin Arewa ta gabas jin dadi da yadda suka sa daukar da lokacin su suna aikin ceton rai a wannan gurin.

Mista Edward Kallon ya bayyana haka ne a sa’ilin da suka shiga yan kunan Arewa ta gabas inda ake fama da tashe tashen hankula na yan Ta’addan Boko Haram.

Ya kuma kara da cewa za a samar da wadacecen guru kwanatar da marasa lafiya domin karban magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *