YAN BINDIGA SUNYI AWON GABA DA MUTANI 17 DAKE SALLA A WANI MASALLACI A NASARAWA

Daga Zubairu M Lawal

A ranar Talata da taga ba ta ne wasu ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai sukayi awan gaba da wasu masallata  daga Masallaci  zuwa daji.

Kimanin mutuani 17 ne yan Bindigan sukayi Garkuwa da su zuwa cikin Daji inda daga bisani suka bukaci a basu kudin fansa naira miliyon 50.

Lamarin ya farune a kauyen Gwargwada-Sabo dake yankin Raya Kasa ta Gadabuke cikin Karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Yan Bindigan sun mamaye Masallacin ne lokacin da ake salla.

Shedu sun tabbatar da cewa cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wasu ma’aikatan dakin adana takardu na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, cikin mata uku da mazaje da akayi awon gaba da su.

Wani mazaunin yankin, mai suna Usman, ya ce lamarin ya faru ne a daren Talata lokacin da Musulmai ke gudanar da sallar Isha’i.

Yana mai cewa ‘Yan bindigar sunyi ta harbe-harbe ta bangarori daban-daban, a dai-dai lokacin da wasun su suka kewaye masallacin, inda sukayi awon gaba da mutanen 17 cikin daji.

Usman yace, maharan sun ware limamin masallacin garin da kananan yara a gefe guda, kafin awon gaba da mutanen.

Iyalan wadanda akayi Garkuwa dasun samu tattaunawa da ‘yan bindigar da suka bukaci naira miliyan daya kan kowane mutun a matsayin kudin fansa, bayan da a ranar farko suka bukaci miliyan 50 kan kowane mutun guda.

Wakilinmu ya tuntubi vangaren Jami’in tsaro inda jami’in hulda da jama’a ta Rundunar yan Sandan Jihar Nasarawa Mista Raham Namsam ya sheda masa ta wayar Salula yace, suma sun karanta labarin ne cikin Jarida amma basu da cikaken labari yan zuwa yanzu.

Shima Shugaban Karamar hukumar Toto Alhaji Nuhu Dauda wanda wakilinmu ya nemi jin ta bakin sa ta wayar Salula,
Ya sheda cewa yanzu haka Gwamnati tana bin duk matakan da ya dace domin kwato mutanin da aka sacen .
Kuma tana kara rarashin iyalan wadanda aka sace wa yan uwa dasu kara hakuru kuma duk abinda sukaji su sanar da Gwamnati

BINDIGA SUNYI AWON GABA DA MUTANI 17 DAKE SALLA A WANI MASALLACI A NASARAWA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *