SARKIN GARAKU YA YABAWA GWAMNA ABDULLAH SULE KAN SAMAR DA ZAMAN LAFIYA

SARKIN GARAKU YA YABAWA GWAMNA ABDULLAH SULE KAN SAMAR DA ZAMAN LAFIYA

Daga Zubairu M Lawal

Sarkin Garaku na Masarautar Abaga Toni Mista Lawrence Sylvestre Ayih ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule saboda yadda yake kokarin daura al’umman jihar da Jihar baki daya bisa tudun muntsira.

Sarkin Abaga Toni na Garaku ya bayyana haka ne a lokacin da Gwamna Abdullah Sule ya kai masa ziyara a fadarsa dake Karamar hukumar Kokona.

Sarkin ya bayyana goyon bayan sa ga Gwamnan ya kuma ummurci “Sarkin Yakin Kokona” ya kara zage dantse wajen ayyukan da yakeyi na cigaban Jihar Nasarawa.

Sarkin ya bayyana jin dadin sa kan ziyarar da Gwamna Abdullah Sule ya kawo masa a fadarsa yau Lahadi .

Ya qara da cewa ya cigaba da yin ayyukan alheri al’umman jihar Nasarawa suna tare da Gwamnan.

Gwamna Abdullah Sule ya nuna godiya da irin goyon bayan da wannan masarauta ta Garaku take baiwa Gwamnatin sa ya kuma yi godiya da saraitar da masarautar ta yi masa na Sarkin yakin Kokona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *