SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KARU YA TAIMAKAWA MATA DA MATASA DOMIN BUN KASA TATTALIN ARZIKI

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KARU YA TAIMAKAWA MATA DA MATASA DOMIN BUN KASA TATTALIN ARZIKI

Daga Zubairu M Lawal

Shugaban Karamar hukumar karu Honorabul Samuel Akala ya taka rawar gani wajen tallafawa mata da matasa da kayayakin Sana’a domin rage zaman kashe wando da bun kasa tattalin arziki a Jihar Nasarawa.

Da yake jawabi a wajen taron rabon kayan Sana’ar Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya yabawa Shugaban Karamar hukumar bisa ga kokarin da yayi na daga darajar Matasan yan kin.

Gwamnan yace tsarin Gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari shine ciyar da matasa gaba a harkokin raya  kasa.

Ya ce Gwamnatin Shugaba Buhari tana baiwa matasa fifiko ta hanyoyi dayawa. Saboda matasa sune cigaban kowata al’umma.

Gwamna Abdullah Sule yayi kira ga matasa da su baiwa Tsarin Gwamnatin Buhari goyon baya saboda cigaban su da kokarin da Shugaba Buhari ya keyi na hanyar daga darajar su a fadin kasan nan.

Ya kuma yabawa Shugaban kasa Muhammad Buhari saboda yadda yake kokarin daura kasan nan zuwa ga tudun mun tsira.

Gwamnan ya jinjinawa Shugaban karamar hukumar Karu Mista Samuel Akala saboda kokarin da yayi na fitar da matasa da mata daga kangin talauci zuwa masu dogaro da kai bisa aikin yi.

Ya kuma yabawa Shugaban karamar hukumar da yadda ya gyara dakin shan magani na Asibitin sha ka tafi dake kauyen Roguwa. Gwamnan ya qara kira ga matasa da su zamu masu dogaro da kai dayin amfani da lokacin su wajen gina kawunan su da cigaban kasa.

Ya jinjinawa Samuel Akala bisa ga baiwa matasa tallafin Mashin 15 domin gudanar da sana’a da mota kirar Sharom guda daya da mata da suka samu Injiniya Nika guda 15, ya ce duk wannan yana cikin tsarin Gwamnati domin tallafawa al’umman jihar Nasarawa.

Gwamnan ya baiwa mata gudumawar naira miliyon biyu  domin gudanar da jali da zai taimakawa rayuwar su.

Shima a nasa jawabin Shugaban karamar hukumar Karu Honorabul Samuel Akala ya jinjinawa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule kan yadda yake taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da hadin kan al’umman jihar.

Ya kuma yabawa Gwamnan jihar kan yadda yake tallafawa marasa galihu da masu galihu wajen Samar da ayyukan yi cikin Jihar.

Ya ce duk abin da zaiyi ya zama kamar koyi ne ga Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule saboda yana ayyukan gina al’umma ta hanyar koyar da su ayyukan yi da basu tallafi lokaci bayan lokaci.

Honorabul Samuel Akala ya godewa al’umman da suka taru a wannan gurin kuma ya bukaci matasa da suke yan kin karamar hukumar Karu cikin jihar Nasarawa da cewa su sani Jihar Nasarawa Jihar ce da kullun take da muradin zaman lafiya.

Kada su bari wasu suyi amfani da su wajen gurbata ayyukan cigaban Gwamnati na samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya kara da cewa karamar hukumar zata cigaba da gina al’umman yan kin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *