BABBAN KOTUN JIHAR NASARAWA TA ZANTAWA IJEOMA OKOLI DA HUKUNCIN KISA

BABBAN KOTUN JIHAR NASARAWA TA ZANTAWA IJEOMA OKOLI DA HUKUNCIN KISA

Daga Zubairu M Lawal

Babban kotun na daya a Jihar Nasarawa wanda mai Shari’a Alkalin Alkalai na Jihar Alhaji Suleman Umaru Dikko ke zama ta yankewa Ijeoma Okoli hukunci kisa.

Hukuncin kisan da aka zantar da shi a yau Littinin wanda katun ta zantar wa Ijeoma Okoli ta sameta da laifin kashe mai gidan ta .

Ijeoma Okoli tana zaune ne a karamar hukumar Nasarawa ta kashe mai gidan ta Innocent Okoli tun a shekarar 2013.

Ijeoma Okoli da mijin ta Innocent Okoli sun haifi yara uku a tsakanin su kafin ta yi ajalin mijin nata zuwa Barzahu.

Kotun ta same Ijeoma da laifi dumu dumu wajen yiwa mijin ta Innocent Okoli kisan gilla.

Ijeoma Okoli mai shekara 47 suna zaune ne da tsohon mijin nata marigayi Innocent Okoli a titin Shagari a garin Nasarawa.

Mai shari’a Sulaiman Umaru Dikko ya ce dokar kasa sakin layi na 221 cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da wannan hukuncin.

Alkalin ya ce hukuncin da shari’a tayiwa Misis Okoli yayi dai dai da laifin da ta aikata. Duk da cewa ta karyata zargin kisan mijin nata tun farko amma bincike ya tabbatar mata da lefinta.

Mai shari’a Alkali Ali shine ya wakilci Kwamishinan shari’a na Jihar Nasarawa Alhaji Abdulkarim Kana yayin gabatar da shari’an a Babban kotu ta daya dake kan titin shanda cikin garin Lafia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *