KU KARANTA – YADDA YAN NIJERIYA SUKA FUSKATA KAN YUN KURIN BA JAMI’AN ROAD SAFETY BINDIGA

‘Yan Twitter sun fusata kan yunƙurin ba jami’an Road Safety bindiga a Najeriya
6 Nuwamba 2020
‘Yan Najeriya da dama sun fusata a shafukan sada zumunta musamman a Twitter tun bayan ɓullar wani labari da ake yaɗawa kan cewa za a fara bai wa jami’an hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya bindigogi.
Jaridar Daily Post a Najeriya ta ruwaito shugaban kwamitin hukumar ta FRSC a Majalisar Wakilai, Akinfolarin Mayowa, inda ya ce ya zama tilas a yi hakan domin tabbatar da an bi doka da oda.
Ya bayyana hakan ne yayin da hukumar ta hallara gaban kwamitin na majalisar domin kare kasafin kuɗinta na 2021 da ta gabatar.
Ya kuma ce kwamitin zai zauna da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha kan wannan batu, da kuma rubuta wasiƙa ga Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari domin aiwatar da buƙatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *