TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA AN DAWO DA GURBIN AL’UMMAN JIHAR NASARAWA

TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA AN DAWO DA GURBIN AL’UMMAN JIHAR NASARAWA

Daga Zubairu M Lawal

Ministan jinkai da bada tallafin ta kasa Hajiya Sadiyya Umar Faruk ta ummurci da a maido da aikin bada tallafi na
Gwamnatin Tarayya cikin gurbin  jihar Nasarawa mai taken Cash Transfer. Kuma ta ba da umarnin a kara yi ma Mutane Rigista.

Ministan jinkai da bada tallafi, Hajiya Sadiya Umar Faruk ta ba da umarnin cewa a dawo da shirin nan na tallafawa al’umman jihar Nasarawa mai taken Cash transfer. Kuma a kara yi ma sabbin mutane jihar Rigista, domin su ci gajiyar wannan shirin na Gwamnatin tarayya a fadin jihar.

Ta ce shirin da aka dakatar da shi a baya sakamakon rashin amincewa da yadda ake gudanar da shirin cikin fadin jihar Nasarawa.

Wanda Gwamnan jihar Injiniya Abdullah Sule ya ya bayyana rashin gansuwarsa da yadda al’umman jihar Nasarawa basu amfana ko kadana da wannan tallafin a wannan lokacin hakan ya sanya aka datakar da bada tallafin har sai an warware matsalar.

Ministan ta qara da cewa jihar Nasarawan tana da mutane Dubu 48, wadanda suke amfana da shirin tun daga 2018, har zuwa 5 ga watan Augusta na 2020 amma an kasa fahintar su waye ke amfana da shi a Jihar.

Rashin gansuwa da yadda ake gudanar da shirin ya sanya aka  dakatar daga hannun shugaban da yake tafiyar da shirin, a sakamakon almundahanan da aka sameshi da shi a wajen gudanar da aikin a wasu kananan hukumomin jihar.

A sakamakon hakan, Gwamnar jihar Nasarawa, injiniya Abdullahi  Sule ya kafa kwamatin bincike, a karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Mista Timothy Anjide, a ranar 17 ga watan Agostan shekara ta 2020 kuma ya ba da report din shi cikin nasara.

Wannan ya sanya Gwamnan jihar Injiniya Abdullah Sule yayi tattaki a ranar Asabar ya gana da Ministan Hajiya Sadaiyya Umar Faruk, aka kuma cimma matsayar dawo da yin ridista domin ba da tallafin ga al’umman jihar Nasarawa.

Gwamna  Abdullah Sule na Jihar Nasarawa tare da Minita Sadiyya Umar Faruk bayan sun kammala tattaunawa a ofishin ta dake Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *