KU BAMU DAMA MU KAWO KARSHEN YAN TA’ADDA A NIJERIYA – KASAR IRAN

KU BAMU DAMA MU KAWO KARSHEN YAN TA’ADDA A NIJERIYA – KASAR IRAN

Jakadan kasar Iran zuwa Najeriya, Ambasada Mohammad Alibak, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa shirye take da taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta’addanci.
Yayinda hirarsa da Nigeria Tribune , ranar Litinin, jami’in diflomasiyyan ya bayyana cewa kasarsa na damuwa kan irin halin tabarbarewan tsaron da ya addabi Najeriya.
Domin kawo karshen haka, ya bayyana cewa “Idan Najeriya ta shirya bamu hadin kai, zamu taimaka wajen kawo karshen ta’addanci a kasar.”

Yace: “Jamhurriyar Musulunci ta Iran ta samu kwarewa mai amfani a wannan fanni sakamakon dogon yakin da tayi da ta’addanci.”
“Tun daga farkon kungiyar ISIS da gwamnatin Amurka ta kirkira, marigayi Qassem Soleimani, na kan gaba wajen yaki da wannan kungiyar.”
“Ka’idar jamhurriyar Iran shine shirye take a koda yaushe domin hada karfi da kasashen da ke fama da matsalar rashin tsaro.”
“Sakamakon haka, mun gana sau tari da jami’an gwamnatin Najeriya kuma mun bayyana musu shirye muke da hada kai dasu kan lamuran tsaro.”

Alibak ya yi wannan jawaban ne ranar cika shekara daya da mutuwar tsohon kwamandan Sojin Iran, Qassem Soleimani.
Shin kuna goyon bayan hakan ko kuwa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *