Gwamnatin Nasarawa ta gabatar da jarabawar Daraktocin da ke son zama Sakatarorin din-din-din

Gwamnan Nasarawa ya kafa kwamitin jarabawan Daraktocin da zasu zamaSakatarorin Din-Din-Din

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya fadi  dalilin da suka sa Gwamnatin sa ta gabatar da jarabawar cancanta ga Daraktocin da ke neman zama sakatarorin  dindindin a jiharNasarawa.

Gwamnan ya jaddada aniyar  cewa matsawar ma’aikaci ya kai ga mukamin ya zama Babban Sakataren Din-din-din a jihar to fa ba makawa sai anyi masa Jarabawa. Domin kafa ginshiki mai karfi ga aikin Gwamnatin farar hula jihar.

Injiniya Abdullah Sule Sule ya bayyana hakan ne ya yin gabatar da rahoton kwamitin da aka tsara don gudanar da jarabawa ga Darektoci don nada su a matsayin Babban sakatarori a ma’aikatar Gwamnati.

Ya ce ya lura  ma’aikatan Gwamnati a yanzu haka suna da rauni, duk da irin ayyukan da Shugaban Ma’aikatan Jihar yake yi, ya sanya muka yan ke  shawarar gudanar da jarabawar cancanta ga Daraktocin da ke son zama sakatarorin din-din-din, domin dawo da darajar aikin Gwamnati yadda ya dace.

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa, tare da ya na yin nadin mukamai a jihar, da sauran abubuwan dubawa, dole ayi al’akari da cancanta bayan jarabawar, domin hakan na da muhimmiyar wajen zaben sakatarorin dindindin.

“Abin da muke kokarin yi, bisa ga ilimin da nake da shi game da gudanar da mulki, duk Wanda za a baiwa jagoranci, dole ya zama mutani ne  da suke da kwarewa a fannin aikin su.

“A wajen zabar, ba wai kawai sakamakon jarabawar ne ake dubawa ba, akwai wasu abubuwan da za a yi la’akari da su dole ne mu samu wakilci daga bangarori daban-daban na jihar. Kuma ba ni da shakkar cewa a duk karamar hukumar da ka je, za a samu kwararu.

Injiniya Sule ya yi amfani da wannan dama ya kuma yi tsokaci a kan jita-jitar da ke cewa gwamnatinsa na kafa kwamitoci da yawa, yana mai jaddada cewa kwamitocin suna da amfani wajen jagorantar gwamnati don yin abubuwa daidai.

“Abu mafi sauki da za a yi ya yin zabar Daraktocin da za su zama sakatarorin din-din-din, shi ne Gwamna ya zauna ya duba duk kan Daraktoci da sauran mutanen da ke ma’aikatan gwamnati ya nada wasu daga cikinsu, kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce “Amma idan ina son yin dai dai, to ya tafi ne ta hanyar kafa kwamitoci saboda mambobin kwamitin sun fi sanin Daraktocin.”

Gwamnan ya ci gaba da ba da tabbacin cewa Gwamnatin sa za ta cigaba da wadannan dabarun biyu, na sanya jarabawar cancanta, tare da yin ishara da mutanen da suka fi kwarewa, a nadin sakatarorin din din din da sauran jami’an gwamnati a wannan matakin, a kalla don jagoranci wanda zai taimakawa gwamnatin jiha ta zama mafi kyau ga jihar.

Gwamnan ya godewa Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Emmanuel Akabe, wanda ya kasance Mukaddashin Gwamna yayin da Gwamnan ya tafi hutu kuma wanda ya hada  mambobin kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Barista Muhammad Ubandoma Aliyu, da kuma mambobin. na kwamitin don yin aiki mai ban mamaki.

Tun da farko, ya yin gabatar da rahoton, Shugaban kwamitin, Jonah Ogbole, ya bayyana mutsin , wanda shi ne irinsa na farko a tarihin jihar, a matsayin juyin juya hali.

Ya yaba wa Gwamnan kan wannan shirin, inda ya kara da cewa, akwai jihohi kalilan a cikin kasar, baya ga gwamnatin tarayya, inda ake tunanin irin wannan kirkirar.

“Muna so mu ba ku daraja a kan wannan. Babban lamari ne, juyin juya hali ne,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *