Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya sun raba kayan abinci a Abuja

Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya sun raba kayan abinci a Abuja

Daga Zubairu M Lawal

Shirin taimakawa marasa galihu da ya samu hadin giwar Gwamnatin tarayya da hukumar rabon tallafin abinci ta majalisar Dinkin Duniya ya yi tasiri ga al’umman yan kin Abuja.

Da yake jawabi a wajen rabon kayan tallafin abincin Babban Darakta a cibiyar rabon abinci na majalisar Dinkin Duniya Dakta  Paul  Howe ya ce wannan tallafin an tanade shi ne domin Talakawa marasa galihu dake bukatar wandama bai kai wannan ba.

Yace yanzu a halin da ake ciki annobar cutar Korona bairus ya durkusar da samun wasu jama’a da dama, yayin da wash  suka rasa ayyuka ko harkan kasuwanci saboda zaman gida a wancan lokacin ya sanya dan jalin su ya kare.

Ya ce cutar Korona ya dakushe hanyoyin tattalin arziki da dama saboda wannan dalilin ne majalisar Dinkin Duniya taga cewa ya dace a duba mutanin dake halin kunci ire-iren wadannan a taimaka masu.

Ya qara da cewa kwamitin da aka samar ta hada da ma’aikatan Gwamnatin tarayya da na hukumar kula da rabon abinci ta majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.

Dakta Paul  Howe, ya ce yanzu a karkashin jagorancin tawagar sa ya kaddamar da nashi aikin daga wadanan yan kunan da suka hada Bwari,  Gwagwalada, da Abuja ta tsakiya . haka zalika sun hada da Karmajiji.

Ya ce wannan tallafin kayan abinci zai kawo sauki cikin rayuwar kunci ga wadanan mabukata da ke rayuwa cikin mawuyacin hali .

Ya Kuma bukaci al’umman yankin da qasa ba ki daya dasu kara zakewa wajen yaki da cutar Korona saboda shine ya kawo mafi munin rayuwar kunci da ake ciki.

Jama’a su dage da yin amfani da takunkumin rufe fuska da wanke hannaye da bada tazara ta wannan hanya ce ka dai za a samu damar kawar da wannan cutar akan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *