Rigakafin cutar Korona yana da mahimmanci ga al’umman Nijeriya- binciken MDD

Rigakafin cutar Korona yana da mahimmanci ga al’umman Nijeriya

Inji MDD

Daga Zubairu M Lawal

Babban mai ba da shawara a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Nijeriya mista Martin Ejidike,  ya bayyana haka.

Ya bayyana mahimmanci yin aluran Rigakafin annobar cutar Korona saboda Rigakafin yafi mahimmanci kan cewa sai mutum ya kamu da cutar sannan ya bukaci magani.

Kiyaye Dokokin yaduwar cutar yana da mahimmanci saboda zaiyi ta siri a cikin al’umma.

Kiyaye dokokin da suka hada da wanke hannaye da safa man hanyaye da rufe fuska suna da mahimmanci saboda suna bada kari ga wanda yake dauki da cutar ko Wanda baya dauke da cutar.

Duk Wanda yake dauke da cutar Korona bairus idan yana amfani da takunkumin rufe fuska da hanci da baki koda yayi atishawa ko tari ba zai yi tasiri akan wanda yake nesa da shi ba.

Saboda akwai kariya daga wannan takunkumin da yake sanye da ita. Wanke hannaye yana rage karfin cutar ga wanda yake dauke da ita koda ya rungume mutum saboda yana wanke hannaye kuma akwai man sinadari na kariya a jikin sa.

Amma mafi alheri bada tazara da rashin shan hannaye yafi komai mahimmanci daga cikin Dokokin kariyer yaduwar annobar cutar.

Yin aluran Rigakafin zai taimaki al’umman kasa wajen yakar yaduwar cutar a fadin kasa cikin al’umma.

Cibiyar yada labarai na ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Nijeriya ta dukufa wajen kara wayar da kan al’umma game da mahimmanci yin aluran Rigakafin.

Mista  Martin Ejidike ya ce idan kashi 70 cikij 100 zasu yi aluran Rigakafin kariyar annobar cutar Korona bairus to za a samu dauki daga yaduwar cutar a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *