An fafata tsakanin kungiyar Nasarawa United da Kano pillars
Daga Zubairu M Lawal Lafia
A ranar lahadin da ta gabata ne aka cigaba da gasar kwallon kafa ta gida Nijeriya gasar da ake kira da suna ( Nigeria Premier League).
An fafata tsakanin kungiyar Nasarawa United da takwararta ta Kano pillars a filin wasa ta Lafia dake bukkan sidi.
Wasan da aka je hutun rabin lokaci babu wanda ya jefa kwallo a ragar wani tsawan minti 45 bayan dawowa hutun Kungiyar Kano pillars ta sauya yan wasa biyu na gaba cikin minti daya da shigarsu sai ga Kwallo a ragar Nasarawa United. Ta kafar Nwagua Nyima.
Ana gab da tashi cikin minti 82 Adamu Hassan ya zura kwallo a ragar Kano pillars inda aka tashi 1-1.
Dukkanin masu horar da yan wasan sun yabawa yan wasan su saboda kwazo da bajintar da suka nuna wajen murza Kwallon .
A filin wasan an tsaurara matakan tsaro na hana yan kallo shiga filin wasan saboda matakan dakile yaduwar annobar cutar Korona bairus.