cikin Daren jiya jami’an tsaro sun kwashe Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna

cikin Daren jiya jami’an tsaro sun kwashe Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami’an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.

Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin.

“Da misalin 12:00 na dare Sojoji da Ƴan sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren,” in ji shugaban makarantar.

Ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa aka kama almajiran ba, amma tun bayan rufe makarantu lokacin ɓullar korona a karon farko, tun lokacin aka sallami ɗaliban makarantar, amma a cewarsa, waɗanda aka kama a yanzu waɗanda suke zaune a gidan Sheikh Dahiru ne ba wai waɗanda suka taso suka zo daga wani gari ba.

Ba za mu iya tantance ko almajirai nawa aka ɗiba ba, domin cikin dare aka zo aka kwashe su,” in ji shi.

Ya kuma bayyana mana cewa sun yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu damar magana da su ba.

Amma ko da BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kaduna, ta shaida mana cewa a halin yanzu ba za su ce komai kan wannan lamari ba, amma nan gaba kaɗan za su fito su yi ƙarin bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *