NA TABBATA GWAMNA ABDULLAHI SULE MUTUMIN KIRKI NE – inji Dr. Kigbu

Gwamna Abdullah Sule mutumin kirkine inji Dr. Kigbu

Daga Zubairu M Lawal

“Gwamna Abdullah Sule mutumin kirkine yana da mutumci kuma ya san darajar mutani baya yaudara ba zai yaudareni ba.

Da Allah na dogara Allah ke bani ci da sha tsawan rayuwa ta.

Na tabbatar da gaskiya Gwamna Abdullah Sule saboda ya rike al’umman Jihar Nasarawa da hannu biyu- biyu. Kuma ya tabbatar da zaman lafiya a Jihar Nasarawa

Ina kira gareku yan uwana yau na tabbatar maku cewa ni Likitan Talakawa Hon.Joseph Haruna Kigbu na koma  Jam’iyyar APC.

Saboda haka dukkanmu maza da mata ko zo muhau jirgin Annabi Nuhu domin samun tsira da cigaban al’umman jihar Nasarawa

Ni daku mutumcin mu yana nan daram. Na sauki hakin da ke kai na na yan gida da uban gida na gaya maku gaskiya daga yau ni Dakta Joseph Haruna Kigbu na bar PDP na koma APC saboda cigaban jihar Nasarawa.

Ban taba yin siyasan ko a mutu ko ayi rai ba. Na tabbatar kuna da mutumci a gareni nima ina da mutumci a gareku idan na zo gari kuna tare dani ko yaushe.

Saboda haka idan abin alheri ya sameku nake zuwa.
kuma idan abin alheri ya same ni kuke zuwa.

Yanzu alheri ya samemu  shi ya sa naga gara na sanar daku saboda mu gudu tare mu tsira tare.”

inji Dr Kigbu yau alhamis da yake ganawa da dukkanin Jami’an yakin niman zaben shi. A gidan sa dake Bukon sidi cikin garin Lafia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *