“BA ZAN YI BARCI DA IDO BIYU BA HAR SAI NA KAWO KARSHEN MATSALAR ALBASHIN KANANAN HUKUMOMI A JIHAR NASARAWA” – GWAMNA A.A.SULE

“BA ZAN YI BARCI DA IDO BIYU BA HAI SAI NA KAWO KARSHEN MATSALAR ALBASHIN KANANAN HUKUMOMI A JIHAR NASARAWA – GWAMNA A.A.SULE”

Daga Zubairu M Lawal

Gwamna Abdullah Sule na  Jihar Nasarawa ya nuna damuwa kan yadda akayiwa Ma’aikatan Kananan hukumonin jihar biyan albashin jeka da halinka.

Gwamnan ya ce abin ta kaici anayiwa Ma’aikatan Gwamnati a matakin Karamar Hukuma ta jihar biyan albashi kashi kashi ko kashi daya bisa dari.

Ya ce ba ya jin daɗin biyan albashi a cikin kashi ɗaya bisa ɗari saboda a duk tsawon rayuwarsa ya kwashe kusan shekara 30, yana aiki bai taɓa karɓar albashin a kashi kashi ba.

Gwamna Abdullah Sule  ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da da masu kula da Bangaren kudi na jihar da suka hada tsofin dakatatun Daraktocin Gudanar da fannin Kudi kamar (DPMs) da  (DFAs) a gidan Gwamnati.

Gwamnan ya ce ba zai samu kwanciyar hankali ba matukar yana ganin Ma’aikatan Gwamnati na karban albshi kashi kashi.

Gwamnan ya jaddada cewa wannan shine karo na farko da ya gana da tsofin masu kula da Bangaren kudi na sha’anin mulki tun bayan da aka dakatar da su. Kuma yanzu ya gayyato sune domin jin ta bakinsu saboda ya gano yadda za a warware wannan matsalar ba tare da cutar da kowa ba.

Gwamnan ya ce tsarin Gwamnatin sa ta baiwa kananan Hukumomi damar cin gashin kanta ta rika aiwatar da duk abubuwan da ya rataya a wuyarta. Amma ba zai ji dadi ba ace Ma’aikatan kananan Hukumomi suna cikin halin kunci a fannin albashi .

Yace a kullun idanuwa na na kan lamurar abubuwan da suka shafi Ma’aikatan Gwamnati domin burina naga komai na tafiya dai dai amma sau dayawa ana samun akasin hakan.

Ya qara da cewa tsawan watanin biyu da aka dakatar da masu kula da vangaren Kudi saboda matsalolin batun biyan albashin ma’aikatan kananan Hukumomi. Duk da cewa tafiyar taku bai amfanar da warware matsalolin ba.

Gwamnan ya bukace su da su baiwa kwamitin da aka kafa hadin kai domin gano yadda za a warware matsalolin dake addabar albashin kananan Hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *