SAMAR DA ZAMAN LAFIYA ZA A SAMAR DA SANSANIN YAN SANDAN KWANTAR DA TARZAMA A LOKO

Sabo da tsaro za a samar da sansanin yan Sandan kwantar da tarzoma ayankin Loko

Gwamna Abdullah Sule

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnan  ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shirye don samar da wani bangare na rundunar ‘yan sandan kwantar da tarzoma na  ta tafi da gidanka, zuwa yan kunan da ke fama da hare-hare yan fashi da makami da Garkuwa da mutani a Qaramar Hukumar Nasarawa.

Gwamna Abdullah Sule ya nuna godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, saboda yadda suka tunkari kawar da matsalar tsaro a yan kin ta hanyar tura Rundunar yan sandan dan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, Gwamnan ya ce jami’an tsaron za su kasance a tsakanin Ajaga, Bakono da Loko, da kuma garin Tunga.

Ya ce  ba da dadewa ba, Sarkin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usman Jibril, tare da Oche Agatu, Alhaji Ahmed Kwanaki Guto, suka ziyarce shi suka bayyana masa damuwar su kan   matsalar tsaro da yake addabar su.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi hanzarin aikewa da ‘yan sanda kwanta da tarzoma , wadanda za a girke a yankin nan da mako guda mai zuwa.

Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mazauna yan kin na Loko da su ba jami’an tsaro hadin kai, ta yadda za su iya kawo kar shen yan ta’addan cikin kankanin lokaci.

Gwamna Sule ya kuma gargadi ‘yan fashin da su bar yan kin, tunda galibinsu sun fito ne daga wasu sassan kasar, yana mai jaddada cewa idan suka gaza barin wurin, abin da ya rage shi ne fatattake su da karfi kamar yadda aka yi a Otu.

Ya qara da cewa wannan ziyarar zuwa  Loko, ta hada da duba Babban Gadan da Kamfanin  Reynolds Construction Company (RCC) ta kammala wanda zai hada jihar da sauran jihohi kuma wajen zai zama babban mahada ga manyan motoci da kanana.

Ya ce har wayau aikin titin da ya hada Mararaba-Udege da Udege-Mbeki mai tsawan kilomita 25 ya cigaba nan ba da dadewa ba za a kammala.

Sarkin Loko  Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya baiwa Gwamna Abdullah Sule matsayin Sarautan Gargajiya na Barayan Loko.

Sarkin ya ce Gwamna Abdullah Sule ya cancanci duk wani irin matsayin da ya ke samu a jihar Nasarawa saboda yadda yake aiki domin cigaban al’umman jihar da tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *