Habaka Ilimi mai daurewa shine abun da muka sanya a gabanmu- Gwamnan jihar Imo

Habaka Ilimi mai daurewa shine abun da muka sanya a gabanmu,

inji Gwamna IMO

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jahar Imo ,Sanata Hope Uzodinma ya bayyana haka lokacin da yake karban bakwancin wata kungiyar mazauna qasar waje da suka shiraya taro kan ingantacen ilumi. Kungiyar mai suna UNESCO tare da UNIC sun ziyarci Gwamna Hope Uzodinma a fadar Gwamnati dake Oware.

Gwamnan ya ce babban aikin dake gabansa shine samar da ingantaciyyar ilumi ga al’umman jihar Imo.

Ya qara da cewa an samu koma baya a vangaren ilumi bayan billowar annobar cutar Korona a Duniya wanda ta shafi Nijeriya harma da jihar Imo.

Ya ce zamuyi kokarin samar da wasu cibiyoyin na musamman da zasu rika bada ilumi a tasiwurar zamani idan aka samu makamancin korona nan gaba.

Idan muna bukatar ganin ilumin ya’yan mu dole mu dauki mataki game da wannan cutar korona shine mu gina wani wajen bada ilimi wanda za’a dinga ilimimantar da mutanen jihar mu kan yadda zasu dinga kaucewa kamuwa da wannan cutar korona bairos.

Gwamnan ya shawarci al’umman jihar Imo da su kasance masu kulawa da dokokin yaki da yaduwar annobar cutar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *