Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin duniya  zasu gudanar da wani zama kan tsarin Abinci

Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin duniya  zasu gudanar da wani zama kan tsarin Abinci

Inji Olusola Idowu

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar majalisar Dinkin Duniya zasu gudanar da wani zama na musamman kan yadda tsarin amfani da Abinci mai gina jiki.

Mista Olusola Idowu wanda shine Babban Sakataren kula da kasafin kudi da yadda za a kashe kudaden a Tarayyar Nijeriya ya wakilci Nijeriya a taron samar da tsarin abinci mai gina jiki da yadda za a raraba su .

Taron mai taken magance matsalolin abinci ta Duniya wanda akayi da Membobin (FSS) Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guttered ya jagoranta .

Mista Olusola Idowu shi ya wakilce Nijeriya a wajen taron ya Kuma bayyana wa manema labarai yadda Nijeriya zata rungume wannan kuddurin wajen samar da nau’in abinci mai gina jiki da zai amfani al’umman kasar daga shekarar 2021 zuwa 2030.

Ya ce Nijeriya zata ginu wajen samar da mahimman abinci da zai amfani al’umman kasar ta, zai kuma basu kariya daga cututtuka ya Kuma basu koshin lafiya.

Ya qara da cewa Allah ya albarkaci Nijeriya da nau’in abinci kala dabam dabam kuma suna da wadacecen kasar noma da komai aka shuka yana tsira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *