Taimakawa kananan Manoma zai farfado da tattalin arziki a Nijeriya-

Taimakawa kananan Manoma zai farfado da tattalin arziki a Nijeriya

Inji  Zainab Shamsuna

Daga Zubairu M Lawal

Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ministan kudi da tsare-tsaren yadda za a kashe kudade ta bayyana yadda za a samu karin tattalin arziki da zai bun kasa a Nijeriya.

Ta ce matukar Gwamnati zata cegaba da tallafawa kanana Manoma masamman na yan kunan Karkara to za a iya samun walwala.

Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a sa’ilin taron hadin giwa da ake farfado da kananan Manoma tsakanin
Gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma kungiyar (IFAD) na Kasashen waje da suke aiki tukuru dan ganin an saukaka samuwar abinci da yaki da yaduwar annobar cutar Korona Bairus. Tace cutar Korona ta taba kowani bangare na tattalin arzikin Duniya hakama fannin Noma da kasuwanci.

Tace hanya dayane za a bi wajen ganin manoma masu karamin karfi da kuma masu rarraba abinci a yankin Arewa maso gabas sun farfado daga kangin talauci.

Itama a nata jawabin Babban Darakta na kungiyar ( IFAD) Misis Nadine Gbossa  (IFAD) sun ware kudi dalar Amurka  da yakai adadin dubu tara ta hannun masu taimakawa manoman karkara dan ganin a karfafasu saboda abubuwan daya shafesu na illar da korona yayi musu.

Ta ce ba manoma kadai ba harma da masu karamin karfi da kuma wadanda suke zaune a karkara a yankunan Arewacin Nijeriya saboda ganin an sake gina wajen da rikice rikice da hare haren yan Ta’adda ya ya lalata.

Misis Nadine Gbossa, itace darakta IFADs’ shiyyar yammaci da kuma tsakiyar Afirika tace taimakon za a yi shine kan Manoma  masu karamin karfi a jahohin Arewa guda bakwai. Kamar jihar Borno da Jigawa da jihar Katsina da Kebbi da  Sokoto da kuma  jihar  Yobe, harma da jihar Zamfara.

Za a kuma cigaba da gudanar da shirin tallafawa Kanana Manoma na karkara daga ofishin Ministan harkan noma da samar da abinci na Nijeriya.

Adadin manoman da zasu amfana a wannan karon  yawan su zai kai 8,000 a yankin Arewacin Nijeriya.

Ministan harkan Noma ta Nijeriya Malam Mohammed  S.  Nanono ya yaba da wannan tallafin na cigaban raya harkan noma.

Ya ce hanaya daya ce ta samar da cigaban al’umman karkara shine harkan noma zai kuma bunkasa tattalin arziki da kasa zata amfana a samu walwala.

Ya qara da cewa qasashen Duniya sun fada cikin damuwar annobar cutar Korona wanda ya durkusar da abubuwa da dama ciki harda harkan noma.

Saboda noma yana cikin tattalin arzikin Duniya. Yayi kira ga manoma su dukufa wajen noma domin samun abinci mai inganci da gina jiki a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *