Dole Gwamnati ta gyara tarbiya da kalaman siyasan batanci saboda zaman lafiyan Nijeriya – MDD

Dole Gwamnati ta gyara tarbiya da kalaman siyasan batanci saboda zaman lafiyan Nijeriya – MDD

Inji Martin EJidike

Daga Zubairu M.Lawal

Babban mai bada shawarwari na kungiyar kare hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya Mista Martin EJidike ;  yayi kira ga babbar murya ga al’umman Duniya Masamman yan Nijeriya da su guji ababen daka iya janyo kashe kashe mara dalili sannan da hanyoyin magance faruwan hakan.

Ya fadi hakanne a wani taro da aka gudanar wanda cibiyar yada labarai Najeriya (UNIC) ta shirya tare da hadin gwiwar cibiyar yada labarai da cigaban al’adu (IACD)  a cikin shekarar 2021.

saboda tunawa da mutanen da suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon kisan kiyashe ko kashe kashe.

Ya kuma bukaci yan Nijeriya da muyi la’akari da irin kalaman muzanta juna ko kabilar juna ko addinin juna wanda hakan ke haifar da fitin tinu cikin al’umma.

attaunawan da akayi an bayyana  dalilin dake janyo haka dole ne a  kyamaci masu irin wannan kalaman  kamar ba da labarai na karya da kuma kalaman batanci da kyamatan addinai da kabilu da akeyi a Najeriya.

Mista Ejidike ya bada shawara cewa tarbiyyan mutane da kuma siyasar batanci da akeyi a  qasar dole sai Gwamnati ta sake fasalinsu domin samar da zamna lafiya.

Idan aka sauya fasalin hakan al’umma zasu fahince juna a kuma samu zaman tare da kaunar juna ta yadda za a samar da dauwamamiyar zaman lafiya a qasar. Inji Dakta   Jide  Jimoh wani Malami mai kula da tsangayar aikin jarida a Jami’ar jihar Lagos.

Ya qara da cewa aibanta kauyen mutum ko aibanta al’adarsa ko kabilansu uwa uba addininsa shi zai hana samun zaman lafiya.

A sakon babban Sakataren Majalisar Xinkin Duniya Mista  Antonio  Guterres ya bukaci al’umma su rika mutumta junansu.

Su mutumta kabila da al’ada saboda kowani mutum da kabilarsa da kuma al’adansa. Babban abinda ya kamata mutani suyi shine su kula da koyarwan addini yadda zasu zauna da juna lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *