Gwamnatin Borno ta taimaka mana wajen samun Ilumi a sansanin gudun hijira

Gwamnatin Borno ta taimaka mana wajen samun Ilumi a sansanin gudun hijira

Inji Zainab Bukar

Daga Zubairu M.Lawal

Dubban matasan da rikici ya shafa a jahar Borno suna samun ilimi kyauta daga Gwamnati, da kuma sana’ar hannu. Wata mata mai 25  mai suna Zainab ta samu karatun a unguwar Kusheri dake cikin garin Maiduguri ta ,jahar Borno.

“Mutanen Maiduguri dake jahar Borno sune suka taimakeni wajen karatun gashi yanzu zan iya rubuta sunana kuma suna taimakon yayana guda hudu idan an basu aikin gida wato (home work)”.

Iyayena basu yadda da ilimin zamani ba, cewar Zainab Muhammad Bukar mahaifiyar yara shida hadda dan karamin danta mai watanni takwas mai suna Muhammad, wanda ke bacci a wajen inda ake koyar damu karatu a karkashin kulawar mai rainon yara (childminder).

Ta ce “Gashi na koyi sana’ar dinkin kaya kuma gashi yanzu na zama mai dinki wanda dashi nake cin abinci a kauyemmu.
Nayi hijira zuwa Maiduguri shekaru biyu da suka wuce bayan mijina ya mutu a wani hari  da aka kawo mana
amma yanzu na sakeyin aure a cikin Maiduguri”.

Zainab ta qara da cewa duk da haka tana son taga ta  koma makaranta kamar domin samun ilumi mai zurfi.

Shide wannan wurin karatn an gina shine a 2019 kungiyar tarayyar tuai tare da hadin gwiwar kungiyar nan mai taimakon yara ta UNICEF  suka bada aikin, Masuyin aikin kuma sune kuma kungiyar masu agazawa yan gudun hijira wanda  rikici ya rutsasu.

Sama da mutane dubu uku da dari takwas ne yan shekaru 15 zuwa 25 sukaci gajiyar wannan aikin daga Monguno, Gwoza, Jere, da kuma Maiduguri.

A Najeruya rikici yafi shafan mutanen Arewa maso gabashin Njjeriya.

A cibiyar koyar da ilimi na Kusheri , sama da mutune dari da masu kanan shekaru wanda basu taba zuwa makaranta ba ko kuma ace wanda karatunsu ya samu tangarda ne dalilin talauci ko kuma rikici da suka tsinci kansu a ciki suke taruwa domin samun ilumi.

Ta kara da cewa bayan koyar damu ilumi ana koyar damu sana’o’in hannu domin dogaro da kai. Akwai fannin sana’o’i dabam dabam. Akwai Kuma Malamai da dama da suke koyarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *