BABU ADALCI A NADIN SHUGABAN GIDAN RADION NBS TA JIHAR NASARAWA – Barde Agwai Lafia

Bamuga  adalci gurin Gwamna Abdullah Sule ba
Inji Barde Agwai Lafia

Daga Zubairu M Lawal

Muhammad Barde Agwai ya kalubalanci Gwamna AbdullahSule na game da ikirarin da ya keyi  na cewa shi mutum ne da yake aiki da akida da gaskiya  amma sai gashi Gwamnan ya nunawa Duniya cewa duk abinda yake fadi ba gaskiya bane.

Yace Gwamna Sule yana ikirarin cewa shi ya zo da akidar da ka’ida da Kuma gaskiya a cikin Gwamnatinsa. Ya ce da gurin taron siyasa da gida da dandali ko ina Gwamna Abdullah Sule yana nuna kan shi a matsayin mutum mai akida da gaskiya amma ba haka bane.

Yace Gwamna Sule ya zo da sabon al’amari a Gwamnatinsa duk mukamanda za a ba da sai anyi sai anyi jarabawa sannan a tantance wanda yake da gogewa.

Duk da cewa al’umma sun amince da wannan kuddurin na Abdullah Sule sai gashi an samu gurbi a ma’aikatan NBS Gwamna Sule ya nada wasu mutani masu kima da nagarta kowa ya san mutanin suna da kima ya sanya su gudanar da jarabawa saboda a samu wanda zai gaji tsohon Shugaban NBS wanda ya samu cigaba zuwa mukamin Sakataren din din din na jihar.

Mutum goma sha daya suka gudanar da wannan jarabawa   Hajiya Hadiza Sarki Dahiru ita tazo na daya.

Sai Gwamna Abdullah Sule ya fito yana fadawa Duniya cewa yana mamakin yadda mutumin garin Lafia ya zo na daya cikin wannan jarabawar. Gwamnan ya kira masu gudanar da jarabawar sun jaddada masa cewa ita tazo na daya

Amma Gwamna Abdullah Sule yace san bayyarda ba, Kuma yana da labarinba a tabayin G.M na NBS kirista a jihar Nasarawa ba.

Wannan ya sanya Gwamna Abdullah Sule yayi tattaki da kanshi zuwa gidan Radio da Talabijin na NBS ya bada sanarwa cewa ya nada Aloko Flashmana matsayin GM.

“Ni da naji haka sai nayi mamaki ganin yadda Gwamnan yake cewa shi mutumne mai Akida da adalci da gaskiya ina batun gaskiyar yana amfani da hakan a matsayin yaudara” inji Barda Agwai.

Kenan babu batun adalci anan babu akida anan babu gaskiya anan. Idan ba yaudara ba ya kamata ace wanda taci jarabawa abata kayanta. Sabodahaka muke ganin Gwamna bayi mana adalci ba.

Kuma a zaman takewa na maabota addinai ba girman Gwamna bane yace ba a tabayin GM kirista a jihar Nasarawa ba. Tunda ba batun addini bane batun aikine Kuma pshi ya sanya aje ayi jarabawa da bai kamata yace yayi jarabawa ba sai ya nada wanda ransa keso babu wanda zai ce saboda me kayi haka ko yace anyi son kai.

Koda manema labarai suka tambayeshi shin yana gani Gwamnan yayi karya kenan ko yayi amai ya lashi game da akidar gaskiya da yake ikirari?

Sai yace “ko banci yayi karya ba to amma bashi da magana daya.

Wata kungiyar matasa mai kumajin kishin Lafia mai suna ( LafiaProgressive Forum) ta fito ta nisanta kanta da al’umman Qaramar HukumarLafia game da maganganun Muhammad Barde Agwai.

Inda ta gudanar da taron manema labarai a ranar laraba a cibiyar yan jaridudake Lafia karkashin jagorancin Hon.Hudu Dahiru Liman.

Suna Kuma juna nuna damuwar su kan fefen bidiyon Muhammad Barde wanda yake maganganu kan nadin sabon Shugaban NBS da GwamnaAbdullah Sule yayi.

Suna danganda Barde da tsohon mukaminshi na Shugaban matasan tsohuwar jam’iyyar shi ta PDP.

Sai dai Muhammad Barde ya ce masu taron manema labarai duk sunafakewane da guzuma domin wani ya sasu ba yin kansu bane.

Kuma akwai maganganu game da yadda ake tafiyar da wannan Gwamnatiwanda aka ki fadin gaskiya lokaci nanan zuwa da za’ayi magana kan salonGwamnatin Abdullah Sule, wanda babu wanda zaiyi musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *