Mutum 42 zasu fuskanci hukunci bayan keta dokar shara a Nasarawa

Mutum 42 zasu fuskanci hukunci bayan keta dokar shara a Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

An kama mutane 42 a jihar Nasarawa bisa zarginsu da kin aiki da dokar tsabtacce muhali a jihar.
Babban Jami’in gabatar da wadanda ke sabawa dokar tsabtacce muhali a gaban kotu Abubakar Mohammed ne ya sanar da haka a Lafia a lokacinda yake amsa tambayoyi daga ‘yanjarida jim kadan da kamala aikin dokar shara a fadin jihar.

Yace wadanda aka kamasu adadinsu yakai 42 sun kuma saba dokar tsaftar muhalli.

Saboda haka za a gabatar dasu gaban kotun tafi da gidanka akwai adadin tarar da za a yi masu daga # 5000 zuwa 10,000 ko kuma zaman gidan yari na tsawan wata shida.

Ya qara da cewa Hukumar ta lika babban kasuwan Lafia taga yadda kasuwar ta lalace da rashin tsafta duk da cewa babu wanda aka samu ya keta doka ya bude shago, amma Hukumar ta yi wa yan kasuwan gargadi su kula da tsaftace kasuwan masamman bangaren da ake yanka kaza da sauran dabbobi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *