Gwamna Sule ya yi kira ga kiristochi da su amfani da koyarwan Al-masiyu wajen tabbatar da zaman lafiya

Gwamna Sule ya yi kira ga kiristochi da su amfani da koyarwan Almasiyu wajen tabbatar da zaman lafiya

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa Injinya Abdullah Sule ya bayyana haka sa’ilin da ya aika da sakon taya al’umman Kiristoci na jihar Nasarawa murnar ranar bikin Easter.

Gwamnan ya bukaci al’umman kiristoci maza da mata dasuyi amfani da irin idu’o’in Yesu Al-masiyyu wajen samar da zaman lafiya a Nijeriya.

Sakon da Gwamnan ya tura ta hannun Sakataren yada labarai Alhaji Ibrahim Addra yayi nuni da mahimmancin wannan rana ga daukacin mabiya addinin kirista.

Ya ce ranace ga duk mabiya addinin kirista ke murna da gudanar da shagulgula saboda haka ya kamata ayi amfani da ranar farin ciki wajen sanya kasar mu cikin adu’a.

Wanda zai wanzar da zaman lafiya a jihar Nasarawa da kuma qasar mu saboda halin da wasu miyagu suke kokarin tsunduma kasar.

Gwamnan yayi kira ga Limaman Coci-Coci da su zaman to masu jaddada koyarwar zaman lafiya tsakanin al’umman da mabiya kowani addini.

Su koyar da mabiya mahimmancin wannan rana ta. Easter saboda darajar ranar da cigaban da aka samu domin yin amfani da koyarwan wanda ake tunawa da shi.

Haka zalika ya bukaci su kiyaye dokokin yaki da yaduwar annobar cutar korona bairus da yake illa ga rayuwar al’umma.

Su kuma yi adu’an Allah ya kawo karshen wannan annobar da matsalolin tsaro baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *