Gwamnan Abdullahi Sule ya inganta harkan kiwon lafiya a jihar Nasarawa – Dr. Ikirama Hasan

Gwamnan Abdullahi Sule ya inganta harkan kiwon lafiya a jihar Nasarawa

Dr. Ikirama Hasan

Daga Zubairu M Lawal

Shugaban Asibitin Dalhatu Araf ta jihar Nasarawa Dakta Ikirama Hasan ya bayyana irin cigaba da aka samu a fannin kiwon lafiya tsawan shekara biyu a mulkin Gwamna Abdullah Sule.

Dakat Ikirama Hasan ya bayyana hakane a sa’ilin da yake zantawa da manema labarai a zauren taro na Asibitin dake garin Lafia.

Dakta Ikirama yace; ba kasafai ake samun Gwamnatin da idan ta kama mulki takan kammala sauran ayyukan Gwamnatocin baya ba.

Amma Gwamna Abdullah Sule da zuwansa yayi kokari wajen kammala ayyukan da ya tarar Gwamnatin baya ta fara bata karasa ba a cikin Asibitin shi kuma ya kammala ya kuma gudanar da wasu aikace aikace nashi a cikin Asibitin.

Gwamnatin Abdullah Sule ta kammala gine ginan dakunan kwanan Ma’aikata ta kuma kammala ofishin ma’aikata da yanzu haka ma’aikata suna cikinta.

Gwamnatin ta kammala dakunan ajiye majinyata da kuma kammala cibiyar Binciken cututtuka.

Ya qara da cewa Gwamnatin Abdullah Sule ta samar da cibiyar binciken cutar Kansan nono na mata, wandsa zai taimakawa al’umman dake ilahirin nahiyar Arewa ta tsakiya.

Ya kuma samar da Na’urorin zamani na binciken cututtuka wanda yanzu Duniya ke amfani dashi domin gano cuta.

Dakta Ikirama yace; yanzu haka Asibitin Danhatu Araf ta tsayu da kafafunta biyu biyu tana gudanar da ayyukan kiwon lafiya domin taimakawa al’umman jihar Nasarawa.

Kuma Asibitin ta samar da hanyoyin koyar da qananan Ma’aikata a fannoni dabam dabam ta yadda zasu zama kwararu nan gaba a harkan kiwon lafiya ba tare da sai sunje karo fahita a wasu jihohi ba.

Sannan Asibitin ta dauki Ma’aikata a fannoni dabam dabam ta yadda yanzu babu matsalar Ma’aikatan jinya da fannin tsaro a cikin Asibitin.

Kuma batun maganar karin girma da kukayi tambaya ana samun korafi amma lamarin ya ta’allakane da cin jarabawa, sannan abune wanda yanzu kungiyar Kwadago take magana a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *