Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya fara biyan 30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya fara biyan 30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin Jihar Nasarawa, ta fara biyan sabon mafi karancin albashin Ma’aikata N30,000 duk da cewa wannan Karin albashin ya takaitane kawai daga matakin 1 zuwa na 6.

Babban Ma’aji na jihar Nasarawa Mista Zakka Yakubu, ya bayyana hakan a ranar Juma’a, yana mai cewa wannan karin albashi zai fara amfanine daga wannan watan na Yuni,

Babban Ma’ajin Yakubu ya bayyana cewa ana cigaba da tattaunawa game da ma’aikatan Gwamnati tun daga mataki na 7 zuwa sama.

Ma’ajin ya bayanin cewa aiwatar da sabon mafi karancin albashin na kasa, ya biyo bayan jerin taruka da kwamitin da Gwamnati ta kafa don duba lamarin, wanda bayan haka aka amince da fara sabon tsarin albashin ga ma’aikatan Gwamnati a kan matakin 1 zuwa 6, kafin tattaunawar ta cigaba ga waɗanda daga matakin 7 zuwa sama.

A bangaren guda, Duk da wannan abin farin ciki da wasu ma’aikatan zasuyi amma da dama na kokawa saboda har yanzu babu batun karin samun matsayi a bakin aiki ga Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Nasarawa tsawon shekara 12 Ma’aikatan Gwamnatin jihar suna tsaye waje daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *