Tsofin Shugabannin APC na yankin Nasarawa ta Yamma sun amince da cancantar Matawalle
Daga Zubairu M Lawal
Tsofafin Shugabannin Jam’iyyar APC a yankin mazabar Sanata ta Nasarawa ta Yamma sun amince da cancantar Barista Labaran Magaji Matawalle.
Tsofin Shugabannin da suka fito daga Gundumomi 55 dake yankin Nasarawa ta yamma sun bayyana Labaran Magaji Matawalle a matsayin Dan Takarar kujerar Sanata ta Mazabar Nasarawa ta Yamma da zai gaji Sanata Abdullah Adamu.
Mazabar Nasarawa ta yamma da ya hada da Karamar Hukuma Keffi da Karu da Kokona da Nasarawa da Toto inda nan ne Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullah Adamu yake wakilta a Majalisar Dattawa ta kasa.
Tsofin Shugabannin APC karkashin jagorancin Hon. Shuaibu Obugye sun tabbatar da amincewa da Matawalle a matsayin wanda zasu zabe ya maye gurbin Sanata Abdullah Adamu a zaben 2023.
Obugye yace; wannan tawagar sun tabbatar da amincewarsu ga Matawalle ne saboda kyawun halayensa da kaunar Jama’a.
Kuma suna da kwarin giwar tallata Matawalle a gurin Jama’an yankin Nasarawa ta yamma.
Yace; kungiyoyin siayasu matasa da Dattawa suna kara bayyana goyon bayansu da Takarar Labaran Magaji Matawalle a matsayin Wanda zai wakilcesu a shekarar 2023.
Alhaji Al-Hasan Obande tsohon Ma’aikacin Gwamnati ne kuma jigone a siyasan yankin ya tabbatar da yadda tafiyar Matawalle take alamun nasara ne.
Jama’a daga yankin Toto da sauransu wannan damace a gareku na ku fito kwai da kwarkwata domin goyon bayan wanda yake taimakonku.
Kungiyar matasa ta Earlier da na Dattawar AFO sun bayyana goyon bayan su ga Takarar kujerar Sanata na Labaran Magaji Matawalle. Sun tabbatar da zaben 2023 lokaci ne da Matawalle zai wakilci yankin Nasarawa ta yamma a Majalisar Dattawa.
Shima Alhaji Abubakar Oyibo wanda ya wakilci al’umman mazabersa ya tabbatar da irin goyon bayan da Matawalle yake samu a wajen Jama’a.