BABBAN ABINDA YASA – Kungiyar Kwadago ta janye yajin aiki a Nasarawa

BABBAN ABINDA YASA – Kungiyar Kwadago ta janye yajin aiki a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Gamayyar kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Nasarawa ta sanar da janye yajin aiki da takwashe tsawan Makonni uku tanayi sakamakon ninman bukatar karin matsayi wajen aiki.

Shugaban kungiyar Kwamared Yusuf Iya yabada sanarwar komawa aiki a ranar Talata 6/7/2021, da gaggawa.

Kwamared Yusuf Iya ya sanar da hakane a yammacin ranar Littinin bayan sanya hannu a takardan yarjejeniyar da kungiyar ta cimma tare da Gwamnatin jihar Nasarawa.

An dai cimma matsaya daya na amincewa da kuddurin da ya sanya kungiyar Kwadago raba goron gayyata zuwa yajin aikin.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da bukatun kungiyar hakan ya sanya Shugabannin kungiyar basuyi jinkiriba suka gaggauta kirar a dawo bakin aiki.

Duk da tsawon makwannin uku da aka kwashe ana kairuwa rana tsakanin Gwamnatin jihar Nasarawa da kungiyar Kwadago. Masu ruwa da tsaki da masu fada aji na jihar Nasarawa sun shiga tsakani, domin sasanta kungiyar da Gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *