Munyi Nadamar Goyon Bayan Buhari, Muna Roƙon Allah Ya Yafe Mana – Gwamna Osun

Munyi Nadamar Goyon Bayan Buhari, Muna Roƙon Allah Ya Yafe Mana – Gwamna Osun

Tsohon Gwamnan jihar Osun Hon. Olagunsoye Oyinlola, ya ce ya yi nadamar marawa Shugaba Buhari baya Tsohon gwamnan ya ce sun yi wa mutane alƙawara da yawa lokacin yankin niman zabe amma ko guba Buhari bai cika ba.
Tsohon Gwamnan ya ce a halin yanzu Allah suke roko ya yafe musu abin da suka yi don ganin Buhari ya hau mulki.

Premium Times ta ruwaito, Tsohon Gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola, ya soki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan rashin magance matsalar tsaro.

Hon. Oyinlola ya yi Gwamna a jihar Osun daga 2003 zuwa 2010 a karkashin jam’iyyar PDP. Ya koma jam’iyyar APC jim kadan kafin zaben Gwamna na 2014 a jihar.

Tsohon Gwamnan Jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola.
Yana ɗaya daga cikin wadanda suka yi wa Shugaba Buhari kamfen gabanin babban zaben 2015.

A hirar da BBC Yoruba ta yi da shi a ranar Alhamis, Mr Oyinlola ya ce wadanda suka marawa Buhari baya tuni sun fara neman gafara daga Allah.

Tsohon Gwamnan ya ce:
“Na taka rawar gani don ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa. Mun yi wa ƴan Nigeria alƙawura masu yawa kuma har yanzu bamu cika ko ɗaya ba. Ɗaya daga cikinsu shine tsaro.
Muna tunanin saboda Buhari tsohon shugaban mulkin soja ne zai kawar da Boko Haram cikin watanni shida amma babu abin da ya canja.

“Obasanjo ya faɗa mana ya san Buhari kuma ya gamsu zai iya jagorancin Nigeria da kyau.

Amma muna tunanin saboda shi tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja ne, zai iya magance matsalar tsaro.

Tun bayan samun ƴanci, da yaƙin basasa, ba a taɓa shiga lokaci mai firgitarwa irin yanzu ba.

“Labarin da muke gani a jaridu kullum shine kisa da sace mutane.
Iyaye a yanzu ba su ra’ayin tura ƴaƴansu makaranta. Tun 1999, ba a taɓa samun tabarbarewar tsaro irin yanzu ba.

Mr Oyinlola wanda ya dawo PDP ya kuma bukaci a sake fasalin mulkin ƙasar yana mai cewa Buhari yana abu kamar bai san alƙawurran da ya ɗauka wa mutane a 2015 ba.

Manema labarai sun yi kokarin tuntubar kakakin Buhari, Femi Adesina, domin jin martaninsa amma bai amsa kira da sakon kar ta kwana ba.

Nigeria tana fama da ƙallubalen tsaro a shekarun baya-bayan nan da suka hada da rikicin makiyaya da manoma, ƴan bindiga, yan ta’adda da sauransu.

Kungiyoyi da dama na kira ga Shugaban Kasa ya sauya tsarin mulkin ƙasar amma kawo yanzu bai ɗauki wani mataki a kai ba. Rashin daukan matakin ya karfafa masu neman ɓallewa daga Nigeria suka ƙara harzuƙa suna neman kafa Biafra da Kasar Yarbawa.

Sai dai tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, da kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila da Bisi Akande da shugabannin APC a Kudu maso Yamma sun soki hakan.
Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa Sun bukaci a haɗa kai a gina ƙasa a ajiye batun kabilanci da addini a gefe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *