Waye ya hana a ba wa Shaikh Zakzaky ‘yancinsa na fita waje neman magani?*

Waye ya hana a ba wa Shaikh Zakzaky ‘yancinsa na fita waje neman magani?*

Tun makonni hudu da suka gabata, babbar kotun jihar Kaduna ta saki jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim. Kotun ta wanke shi tas, a kan bai aikata laifin komai ba. Amma har yanzu ba su samu damar fita kasar waje domin neman magani ba, saboda jami’an tsaron Nijeriya na rike da fasfo din su na kasa da kasa, kuma an ki a sabunta musu fasfo din, domin su samu damar fita waje neman magani.

Hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da Hukumar jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun musanta cewa fasfo din kasa da kasa na Shaikh Zakzaky da matarsa yana hannunsu. Kamar yadda kowa ya sani, a lokacin da babbar Kotun jihar Kaduna ta ba da umarnin a bar Shaikh Zakzaky ya tafi kasar Indiya domin neman magani, suna sauka daga jirgi jami’an tsaron Nijeriya suka kwace dukkan takardunsu na tafiye-tafiye. To waye suka ba wa? Wannan ba wani abu ba ne da ya dauki lokaci da za a ce an manta wanda aka ba wa. Shin an ba da wadannan fasfo na kasa da kasa ne ga wasu manyan mutane a cikin gwamnati, kamar yadda ake hasashe, wadanda ke amfani da ikonsu da tasirinsu don kara tsare Shaikh din da matarsa ​​ta hanyar hana su ‘yancin da kotunan kasa suka ba su? Muna fatan wannan ba wani mugun makirci ne na wadanda ke da iko cikin masu mulki a Nijeriya don hana ma’auratan samun damar fita jinya kasar waje ba.

Muna son tunatar da jama’a cewa kusan shekaru shida da suka gabata, rahotannin likita suna nuna cewa yanayin lafiyarsu yana kara tabarbarewa ne, don haka suna bukatar tafiya zuwa kasashen waje don neman magani. Wannan shi ne ma dalilin da ya sa babbar kotun jihar Kaduna ta ba su hutun jinya wanda daga baya gwamnati ta soke shi a shekarar 2018.

‘Yan’uwa Musulmi maza da mata na Harkar Musulunci da sauran masu son adalci a fadin duniya na sake samun damuwa, saboda irin wadannan abubuwa masu tayar da hankali da suka hada da abin da ya sanya gwamnatin Buhari ta tsare mutanen biyu. Don haka, muna kira ga kasashen duniya da su yi kira ga gwamnati a kan ta saki fasfo din Shaikh Zakzaky da matarsa. Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta saki musu fasfot din su ko ta ba su sabbi, wanda hakan zai ba su damar tafiya asibitin da suke so ba tare da wani bata lokaci ba.

Saka Hanu:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKA ISLAMIYYA A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *