An bukaci Gwamnatin Nijeriya data rika rabon mukamai ga mata Inji Amina Muhammad

An bukaci Gwamnatin Nijeriya data rika rabon mukamai ga mata

Inji Amina Muhammad

Daga Zubairu Lawal

Maitaimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad tayi kira ga masu fada aji na mukaman siyasa a Gwamnatin Nijeriya dasu rika rabon mukaman kujeran Gwamnati ga mata.

Hajaiya Amina Muhammad tace mata suna taka mahimmiyar rawa a siyasan Nijeriya musamman lokacin zabe da yakin niman zabe.

Amma da zarar an kafa Gwamnati to maza suke amfana da dukkan mukamana Gwamnati kashi 90% a harkokin Nijeriya.

Tace; kamata yayi a samar da gurabe da yazamana mukaman na matane na dindindin.

Ko Kuma a raba duk mukamai kashi 38% cikin 100 mata su amfana da kashi 38 domin samar da harkokin cigaban siyasan Nijeriya.

Hajaiya Amina Muhammad tace; a bangaren zababun kujerun mulki mata sukan samu tsaiko. Ba a cika samun mata da suke samun nasara a zabe ba.

Ya kamata ace mata suna samun nasara mai inganci ga kujerun da ake zaben, daga matakan Kananan Hukumomi zuwa Jihohi zuwa Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *