An bukaci Gwamnatin Nijeriya data rika rabon mukamai ga mata – Amina Muhammad

An bukaci Gwamnatin Nijeriya data rika rabon mukamai ga mata – Amina Muhammad

Daga Zubairu Lawal

Maitaimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad tayi kira ga masu fada aji na mukaman siyasa a Gwamnatin Nijeriya dasu rika rabon mukaman kujeran Gwamnati ga mata.

Hajaiya Amina Muhammad tace mata suna taka mahimmiyar rawa a siyasan Nijeriya musamman lokacin zabe da yakin niman zabe.

Amma da zarar an kafa Gwamnati to maza suke amfana da dukkan mukamana Gwamnati kashi 90% a harkokin Nijeriya.

Tace; kamata yayi a samar da gurabe da yazamana mukaman na matane na dindindin.

Ko Kuma a raba duk mukamai kashi 38% cikin 100 mata su amfana da kashi 38 domin samar da harkokin cigaban siyasan Nijeriya.

Hajaiya Amina Muhammad tace; a bangaren zababun kujerun mulki mata sukan samu tsaiko. Ba a cika samun mata da suke samun nasara a zabe ba.

Ya kamata ace mata suna samun nasara mai inganci ga kujerun da ake zaben, daga matakan Kananan Hukumomi zuwa Jihohi zuwa Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *